Zaben Bayelsa
Wani ma’aikacin hukumar INEC da aka yi ram da shi a ranar jaji-birin zaben Gwamnonin jihohi, ya samu ‘yanci. Sanarwa ta fito daga INEC cewa malamin zaben ya tsira.
Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) sun kama wasu mutane 14 da ake zargi da sayen kuri’u a rumfunan zabe a Bayelsa da Imo.
PDP da APC sun sha gaban juna a Bayelsa da APC, inda zaben Kogi yayi zafi tsakanin tsakanin Ahmed Usman Ododo da Murtala Yakubu Ajaka daga kabilun Ebira da Igala.
Rahotanni sun nuna cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun farmaki wasu rumfunan zabe a jihar Bayelsa, inda suka sace kayayyakin zabe bayan bude wuta.
Bayanai da suke fitowa sun nuna cewa Hukumar Zabe mai Zaman Kanta (INEC) za ta fara tattara sakamakon zaben gwamnan Kogi da Bayelsa gobe Lahadi 12 ga watan Nuwamba.
Yanzu nan labari ya zo cewa Hukumar INEC ta bada sanarwar dakatar da zaben sabon gwamna a wasu daga cikin bangarorin jihar Kogi kamar yadda wasu su ke kira.
Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya lashe akwatin zabensa a zaben gwamna na jihar Bayelsa da ke gudana a yau Asabar 11 ga watan Nuwamban shekarar 2023.
Al'umma suna nan sunyi zugum suna jiran ganin yadda za ta kaya a yayin da hukumar zabe INEC ke shirin gudanar da zabukan gwamba a jihohin Kogi, Bayelsa da Imo.
A yayin da ake gudanar da zabukan zabe a jihar Bayelsa, wasu masu zabe sun yi zargin jam'iyyar APC da PDP suna siyan kuri'u daga masu zabe a wasu yankuna.
Zaben Bayelsa
Samu kari