APC
Gwamnan jihar Niger, Mohammed Umar Bago ya tallafawa dalibai da ke karatu a Jami'ar Abdulkadir Kure da ke jihar inda ya rage kaso 50 na kuɗin da suke biya.
Jami'yyar APC a Zamfara ta zargi Gwamna Dauda Lawal ta lalata tsaron jihar saboda rashin hada kai da karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle wurin dakile matsalar.
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya soke daukar ma'aikata 10,000 da Nyesom Wike ya yi a karshen mulkinsa inda ya zargi rashin bin tsari a daukar ma'aikatan.
Shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Abdullahi Ganduje ya ce tun yanzu tsare-tsaren da Bola Tinubu ke dauka sun fara haifar da ɗa mai ido a cikin shekara daya.
Ministan ayyuka, Dave Umahi ya koka kan yadda ƴan siyasa ke cin amanar iyayen gidansu wadanda suka taimake su wurin tabbatar da sun lashe zabe a jihohinsu.
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Abuja ta sanya ranar, 13 ga watan Yuni domin fara sauraron karar da ke neman a tsige Ganduje daga shugabancin APC.
Wata babbar kotun jiha da ke birnin Makurdi ta dakatar da Gwamna Alia Hyacinth na jihar Benue game da binciken tsohon gwamna, Samuel Ortom daga 2015 zuwa 2023.
Tsohon dan majalisar wakilan Najeriya, Tajuddeen Yusuf ya ce abu ne mai matukar wahala Atiku Abubakar da Peter Obi su hade guri guda domin tunkarar zaben 2027.
Mataimakin shugaban jam'iyyar APC a yankin Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya soki tsoma baki da Gwamnatin Tarayya ta yi a rikicin sarautar Kano.
APC
Samu kari