Anambra
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yabawa gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo kan ayyukan ci gaba da yake gudanarwa a jihar. Ya ce yana da hangen nesa.
An tsaurara tsaro a Anambra gabanin ziyarar Tinubu. Ana sa ran shugaban kasar zai ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin jihar ta kammala.
Kwamishinar jin dadin mata ta jihar Anambra, Ify Obinabo, ta bayyana yadda wata mata ta zo ofishinta tana neman taimako kan yadda ɗanta ke yi wa mata ciki.
Jam'iyyar LP ta samu nakasu a jihar Anambra. Makusancin dan takarar shugaban kasa na LP a zaben 2023, Peter Obi, Oseloka Obaze ya yi murabus daga jam'iyyar.
Tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano ya ce Fafaroma Francis mutum ne mai saukin kai kuma cike da alheri, ya tuna kyautar hula da ya bashi a Vatican a 2020.
Wanda ya yi takara a zaɓen fitar da gwani da gwamna a Anambra karkashin APC, Valentine Ozigbo ya maka jam’iyyar a kotu kan zaben, yana neman soke sakamakon.
Rundunar yan sandan jihar Anambra ta bayyana cewa an cafke wani mutum mai shekaru 49 da ake zargi da hallaka mahaifiyarsa saboda sabani a kan kudin kasuwancin rogo.
Shugaba Tinubu ya nada Chief Basil Ejidike a matsayin shugaban hukumar gudanarwar NRCRI. Tinubu ya ce yana da kyakkyawan yakinin cewa Ejidike zai yi aiki tukuru.
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar babban jigon jam'iyyar APGA, Maja Umeh ranar Laraba, 9 ga watan Afrilu, 2025, ya mutu yana da shekara 64 a duniya.
Anambra
Samu kari