
Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso







Tsohon kwamishina a jihar Kano, Musa Ilyasu Musa Kwankwaso ya gargadi shugabannin jam'iyyar da su yi taka tsan-tsan kan shirin shigowar Sanata Rabiu Kwankwaso.

Musa Iliyasu ya yi zargin cewa madugun Kwankwasiyya na ƙoƙarin shiga jikin Tinubu ba don komai ba sai don samun mafakar da Abba zai samu zarcewa zango na 2.

Rabiu Musa Kwankwaso ya fadawa ‘Yan majalisar tarayya abin da za su yi a kan kudirin haraji. Kwankwaso ya na so ‘yan majalisar jam’iyyar NNPP su yaki kudirin.

Dakta Musa Iliyasu Kwankwaso ya yabawa Tinubu kan aikin titin Kano-Kaduna-Abuja, bututun AKK, da aikin dam din N95bn. Ya yi godiya kan nadin da aka yi masa.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada mukamai kusan 100 a hukumomin raya tafkin ruwan Najeriya 12 a Kudu da Arewa. Mutane 72 sun samu mukamai a jihohi.

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Musa Ilyasu Kwankwaso da Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi a hukumar raya kogunan Hadejia-Jama’are a Najeriya.

Hon. Musa Iliyasu ya ce Sanata Rabiu Kwankwaso ne babbar matsalar Kano ba Abdullahi Ganduje ba, yana mai cewa NNPP ta raba kanta da wasu 'yan siyasar jihar.

Mai taimakawa gwamnan Kano, Salisu Yahaya Hotoro, ya yi magana a kan tsige Abdullahi Baffa Bichi. Abba Kabir Yusuf ya yi waje da Abdullahi Baffa Bichi.

Jigo a jam'iyyar APC, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bukaci kungiyar ACF da ta daina sukar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan matsalolin Arewacin Najeriya.
Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso
Samu kari