Aikin Hajji
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya mika mulkin jihar ga mataimakinsa domin tafiya kasa mai tsarki gudanar da aikin Hajjin 2024.
Hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta sanar da cewa za ta kammala jigilar maniyyatan Najeriya a ranar Litinin, 10 ga watan Yunin 2024 zuwa kasa mai tsarki.
Biyo bayan yawaitar mutuwar mahajjata a kasar Saudiyya saboda tsananin zafi, an dauki matakan sanyaya yanayi domin rage mutuwar mutane yayin aikin hajji.
Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kebbi ta tabbatar da rasuwar wani Alhaji a birnin Makkah na kasar Saudiyya. Alhajin ya rasu ne bayan 'yar gajeruwar jinya.
Hukumomi a kasar Saudiyya sun tabbatar da cewa wata mata mai suna Hajiya Hawawu daga Kwara ta rasu, binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa ta yi ajalin kanta.
Gwamnatin jihar Kano ta samar da asibiti a kasa mai tsarki domin duba Alhazan jihar masu gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024 a Saudiyya.
Kungiyar Concerned South-South Muslims da ke Kudu maso Kudu ta bukaci Bola Tinubu kan sauya sunan wakiliyar hukumar NAHCON a yankin, Zainab Musa.
Maniyyatan aikin hajjin bana daga jihar kwara sun yi zanga saboda sauke rashin tashi da su da zuwa kasa mai tsarki domin sauke farali. Gwamnati ta ba su hakuri.
Gwamnatin jihar Kano ta ƙara ɗaukar matakai da nufin inganta walwala da jin daɗin alhazan jihar na tsawom lokacin da za su ɗauka a ƙasa mai tsarki.
Aikin Hajji
Samu kari