Aikin Hajji
Kungiyar 'yan jarida ta IHR ta jinjinawa hukumar jin dadin alhazai a jihar Kaduna bayan dawowa mahajjata kudi kimanin $50 saboda sauki da aka samu kan hadaya.
Jirgin farko da ya kwaso alhazan Najeriya daga Saudiya ya Iso gida. Kashi na farko na alhazai 410 daga jihar Kebbi da suka yi aikin Hajjin bana sun dawo gida.
Mai gadi da ke rike da makullin Ka'abah, Dakta Saleh Bin Zain Al-Shaibi ya rasu da safiyar yau Asabar inda aka yi sallar jana'izarsa a Masallacin Harami.
Rahotanni sun bayyana cewa Ƙasar Masar ta rasa alhazai 600 waɗanda suka rasu sakamakon tsananin zafin da aka yi fama da shi a aikin hajjin bana a Saudiyya.
Alhaji daga jihar Jigawa ya ƙara ɗaga kimar Najeriya yayin da ya mayar da jakar kuɗin da ya tsinta a Masallacin Annabi SAW a Madinah, ya yi cigiya bai ga mai ita ba.
Najeriya ta sake babban rashi bayan rasuwar Hajiya a kasar Saudiyya mai suna Ramota Bankole wacce ta kasance jajirtacciya a jam'iyyar APC da ta rike mukamai.
Hukumar kula da alhazai ta jihar Kaduna ta bayyana cewa za ta mayarwa wadanda su ka biya kudin aikin hajji ta hukumar su 700 kudin ragon layyarsu.
Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta hana mahajjata dauko ruwan ZamZam daga Saudiyya yayin da suke dawowa gida Najeriya. Hukumar ta ce za a ba su idan sun iso.
Sama da musulmi 900 ne su ka kwanta dama yayin aikin hajjin bana, yayin da mutane da yawa ke neman ‘yan uwansu da aka nema aka rasa a kasa mai tsarki.
Aikin Hajji
Samu kari