Abun Al Ajabi
Wata mata da ke kan hanyarta na zuwa wani wuri mai matukar muhimmanci ta fado daga kan achaba sannan ta jike jagab da ruwan kwata. Bidiyon ya yadu a soshiyal midiya.
Jama'a sun shiga mamaki bayan gano yadda budurwa ta kammala digiri mai dauke da taragon da babu kamarsa a wannan zamani da ake karatun boko da wuya
Wata budurwa ta bayyana yadda ta tashi kan samari da wani nau'in kitso mai sauki kuma na gargajiya da mata ke yi tun zamanin baya can ba yanzu ba.
Wata matar aure yar TikTok ta gwangwaje mijinta da kyaututtuka na miliyoyin naira, matar ta cika da murna yayin da ta baje kolin kayayyakin da ta siya masa.
Gambo Haruna, wata bazawara da mijinta ya mutu shekaru shida da suka gabata bayan fama da rashin lafiya, tana sana’ar tura baro domin ciyar da yaranta shida.
Wata mata wacce ke fama da lalurar tabin hankali ta haifi kyakkyawan jinjiri mai ji da lafiya kuma hotunan sun yadu bayan an wallafa shi a Facebook.
Gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya kai ziyarar bazata ga tsohon telan da ke yi masa dinki a lokacin da yake karatu a jami’ar jihar Ekiti a ranar Juma'a.
Wani mutum da ake zaton lauyan bogi ne ya je kotu kuma yak are mutane sannan ya yi nasara a kararraki 26. An yi zargin cewa ya yi wa wani lauya sojan gona ne.
Wata uwa yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta nuna gagarumin sauyawar da danta ya yi. Jama’a sun mato tare da jinjina kyawunsa.
Abun Al Ajabi
Samu kari