"Ba Mu Bukatarka," Gwamna Bala Ya Samu Gagarumar Matsala a Shirinsa na Komawa APC

"Ba Mu Bukatarka," Gwamna Bala Ya Samu Gagarumar Matsala a Shirinsa na Komawa APC

  • Mambobin jam'iyyar APC na ci gaba da nuna adawarsu da shirin sauya shekar Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi
  • Wata kungiyar 'yan APC a jihar Bauchi ta tura wasikar koke ga shugaban jam'iyya na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda
  • Kungiyar ta bayyana dalilai 10 da ya sa ba ta goyon bayan sauya shekar Gwamna Bala, ciki har da batun sukar gwamnatin Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed na ci gaba da fuskantar matsaloli a yunkurinsa na sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Tun bayan bullar labarin cewa Gwamna Bala (Kauran Bauchi) na shirin komawa APC, jiga-jigan jam'iyyar musamman a jihar Bauchi suka fara nuna adawa da hakan.

Gwamnan Bauchi.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed a fadar gwamnati Hoto: Sen. Bala Mohammed
Source: Twitter

Gwamna Bala na fuskantar tangarda

Kara karanta wannan

Za a jika wa APC aiki, tsohon jagoran yakin neman zaben Tinubu a Zamfara ya koma ADC

Jaridar Leadership ta rahoto cewa wata kungiya ta 'yannAPC a Jihar Bauchi ta bayyana cewa ba ta goyon baya ko maraba da Gwamna Bala, zwwa cikin jam'iyyar.

Kungiyar ta bayyana rashin amincewarta a fili kan zargin da ake yi na cewa yana shirin sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Kungiyar mai suna, "APC Solidarity Group & Allied Associations" ta Jihar Bauchi, ta bayyana matsayinta ne a ranar Asabar cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai.

Kungiya ta aika wasika ga shugaban APC

Sanarwar ta bayyana cewa sun riga sun aika koke ga Shugaban APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, inda suka jero dalilai guda 10 na rashin amince wa gwamnan ya shiga jam'iyya.

"Yayin da babban zaben 2027 ke gabatowa, ya zama dole mu kiyaye karfin jam'iyyar APC, mutuncinta, da kuma hadin kan cikinta a Jihar Bauchi.
"Dangane da wannan, muna so mu gabatar da wadannan damuwoyi namu kan yuwuwar karbar Sanata Bala Mohammed Abdulkadir a jam'iyyarmu," in ji kungiyar.

Dalilan 'yan APC na juya wa gwamnan baya

Yayin da take lissafa korafe-korafenta, kungiyar ta bayyana abin da ta kira yawan sukar da gwamnan ke yi wa jam'iyyar APC da kuma gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fili.

Kara karanta wannan

Rigima ta kunno kai a APC bayan gwamna ya nuna sha'awar sauya jam'iyya a Najeriya

Haka kuma, kungiyar ta yi nuni da abin da ta kira raguwar farin jinin gwamnan a wurin jama'ar Jihar Bauchi, da kuma adawar siyasa da ke tsakaninsa da manyan jiga-jigan APC, cewar rahoton Daily Post.

Tutar APC.
Tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: APC Nigeria
Source: Getty Images

A cewarta, Gwamna Bala ba ya shiri da kusoshin APC kamar tsohon gwamna Isa Yuguda, tsohon Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara, Tsohon Ministan Harkokin Waje Yusuf Tuggar, da kuma Sanata Shehu Buba Umar.

Ta yi gargadin cewa barin gwamnan ya shiga APC na iya haifar da rashin tabbas a cikin gida, sannan ya kara raba kan yana jam'iyyar a Jihar Bauchi, tare da jawo nakasu a zabe na gaba.

Gwamnan Bauchi ya kori kwamishinan tsaro

A baya, kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed ya sallami kwamishinan tsaron Bauchi, Alhaji Ibrahim Gambo Galadima daga mukaminsa a wani dan karamin garambawulda ya yi.

Sanarwar sallamar kwamishinan daga aiki ta fito ne ta hannun mai magana da yawun gwamnan jihar Bauchi, Kwamared Mukhtar Gidado.

Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin shigo da sababbin dabarun gudanar da mulki da inganta tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262