"Allah na Fushi da Kwankwaso," NNPP Ta Fadi Dalilin Rikicin da Ya Taso a ADC

"Allah na Fushi da Kwankwaso," NNPP Ta Fadi Dalilin Rikicin da Ya Taso a ADC

  • Sakataren NNPP na ƙasa, Ogini Olaposi, ya bayyana cewa fushin Allah ne ke damun ADC saboda karɓar Sanata Rabiu Kwankwaso da Buba Galadima
  • Jam'iyyar ta zargi Kwankwaso da ƙoƙarin ƙwace NNPP ta bayan fage yayin da ya sauya mata tambari da launi ba tare da izinin shugabanni ba
  • NNPP ta ba ADC shawarar cewa lallai Kwankwaso ya nemi gafarar mambobin jam'iyyarsa ta asali idan har suna son samun zaman lafiya a yanzu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Jam'iyyar NNPP ta fito fili ta ɗaura alhakin rikicin shugabanci dake addabar ADC a wuyan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma babban jigon siyasa Buba Galadima.

Wannan martani na zuwa ne bayan da hukumar INEC ta janye amincewa da shugabancin David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaba da sakataren ADC, biyo bayan umurnin kotun ɗaukaka ƙara.

Kara karanta wannan

NNPP ta fadi zunubin Kwankwaso a siyasa, ta tausayawa jam'iyyar ADC

NNPP ta ce jam'iyyar NNPP ta fada cikin rikici ne saboda fushin Allah na bibiyar Kwankwaso
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso rike da katinsa na zama cikakken dan jam'iyyar ADC. Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

NNPP ta zargi Kwankwaso da cin amana

NNPP ta bayyana cewa ba abin mamaki ba ne ganin yadda ADC ta tsinci kanta a wannan yanayi, kamar yadda rahoton Vanguard ya nuna.

A cikin wata sanarwa da sakataren NNPP na ƙasa, Ogini Olaposi ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa Kwankwaso da mabiyansa na Kwankwasiyya sun shigo NNPP ne a 2022 kyauta domin yin takara, amma daga baya suka yi ƙoƙarin ƙwace jam'iyyar.

"Babban laifinsu ga Allah shi ne sauya tambari da launin NNPP ba tare da amincewar shugabannin jam'iyyar na asali ba," in ji sanarwar.

"Allah na fushi da Kwankwaso" - NNPP

NNPP ta ƙara da cewa Allah ya yi fushi da jam'iyyar ADC ne saboda karɓar Kwankwaso ba tare da ya nemi gafarar waɗanda ya yi wa ba daidai ba a jam'iyyar da ya bari.

Ta jaddada cewa ba jam'iyyar APC ko INEC ba ne ke da alhakin halin da ADC take ciki, face "fushin Allah" ne dake bibiyar Kwankwaso a yanzu.

Kara karanta wannan

EFCC za ta jika wa Malami aiki, ta jero kadarori kusan 60 da ake so kotu ta kwace

Jam'iyyar NNPP ta gargaɗi ADC da kada ta bari ta sha wahala saboda laifin wani daban, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

Jam'iyyar NNPP ta ce Kwankwaso ne ya jawo duk rikicin da ADC ke fuskanta a halin yanzu.
Tutar jam'iyyar NNPP. Hoto: UGC
Source: UGC

Shawarar NNPP ga jam'iyyar ADC

Ta ba su shawarar cewa idan har suna son fita daga wannan matsalar, to dole ne Kwankwaso da Buba Galadima su je su nemi afuwa tare da yin sulhu da shugabannin NNPP na asali.

Haka kuma, sanarwar ta zargi Kwankwaso da rashin iya sarrafa magoya bayansa, inda ta bayyana cewa yawancin mabiyansa a zahiri masu goyon bayan APC ne daga yankin Kudu-maso-Yamma.

NNPP ta jaddada cewa muddin ba a nemi gafara ba, to matsalolin siyasa za su ci gaba da addabar duk inda Kwankwaso ya sa ƙafa.

An gano matsalar da ADC ta samu

A wani labari, mun ruwaito cewa, Cif Femi Fani-Kayode ya bayyana halin ni 'ya su da jam'iyyar hamayya ta ADC za ta shiga gabanin babban zabe mai zuwa.

Kalamansa na zuwa ne bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta soke sunan David Mark daga matsayin Shugaban ADC.

Femi Fani-Kayode ya bayyana cewa tabbas, ADC na iya fuskantar matsala wajen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa da INEC za ta aminta da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com