An Fara Watsewa daga APC, Tsohon Ministan Najeriya Ya Raba Hanya da Tinubu
- Rahotanni sun nuna cewa tsohon ministan shari'a, Michael Aondoakaa ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki
- Michael Aondoakaa ya ce matakin na da nasaba da halin da ake ciki a siyasa da kuma kare muradun al’ummar jihar Benue
- Sai dai duk da matakin da ya dauka, ya yaba wa Bola Tinubu tare da alƙawarin cewa zai sanar da matakin da zai dauka a gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Michael Aondoakaa, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC.
Ya ce ya ɗauki wannan mataki ne bayan tunani mai zurfi da kuma tattaunawa mai faɗi da iyalansa, abokan siyasa da magoya bayansa.

Source: Twitter
The Cable ta wallafa cewa Michael Aondoakaa ya sanar da fita daga APC ne a cikin wata sanarwa, inda ya ce ficewarsa daga jam’iyyar ta fara aiki ne daga ranar 28 ga Maris, 2026.
Bayanin Aondoakaa kan fita daga APC
Aondoakaa ya nuna godiyarsa bisa damar da aka ba shi ya yi aiki da kuma ba da gudunmawa wajen bunƙasa jam’iyyar a matakai daban-daban a baya.
Sanarwar ta ce:
“Halin da ake ciki a yanzu ya sa ya zama dole ya ɗauki wannan mataki domin amfanin al’ummarsa da kuma darajar dimokuraɗiyya.”
Ya kuma gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa jagorancin da ya yi da kuma kulawar da jihar Benue ta samu a gwamnatinsa.

Source: Facebook
Bayani kan Sanata George Akume
Haka kuma, ya yabawa Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume bisa jagorancin da yake bayarwa ga jam’iyyar APC a jihar Benue.
Rahotanni sun nuna cewa ya ce yana girmama rawar da Akume ya taka wajen tsara siyasar jihar, tare da jaddada cewa zai ci gaba da mutunta shi.
Aondoakaa ya kuma gode wa shugabanni da ‘ya’yan jam’iyyar a ƙaramar hukumar Ushongo, da ma dukkan jihar Benue da sauran wurare bisa goyon baya da haɗin kai da suka ba shi tsawon shekaru.
Kiran Aondoakaa ga magoya bayansa
Rahoto jaridar Vanguard ya nuna cewa Aondoakaa ya bukaci magoya bayansa da su kasance masu natsuwa, zaman lafiya da kuma jajircewa.
Ya ce:
“Akwai sabon shiri da nufin ceto da sake gina jihar Benue domin amfanin al’umma, wanda za a bayyana nan gaba,”
Bayanai sun nuna cewa Aondoakaa ya taba rike mukamin ministan shari’a da babban lauyan gwamnatin tarayya daga shekarar 2007 zuwa 2010.
Fatan da ake wa Tinubu bayan tazarce
A wani rahoton, kun ji cewa Sarkin Iwo, Oba Abdulrashid Akanbi ya sanar da cewa 'yan Najeriya za su ci moriyar gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya bayyana haka ne a wani sako da ya fitar domin taya shugaban murnar cika shekara 74 da haihuwa, inda ya masa fatan samun nasara.
Oba Akanbi ya ce akwai alamun 'yan Najeriya za su ji dadi a mulkin Tinubu har su bukaci a ba shi damar wuce wa'adi na biyu bayan ya yi tazarce.
Asali: Legit.ng

