Rigima Sabuwa: Matakin da Shugaban PDP Ya Daukai bayan Kotu Ta Umarci a Cafke Shi
- Shugaban tsagin jam'iyyar PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki, ya shiga cikin matsala bayan wata kotu ta ba da umarnin a cafke
- Alkalin kotun ya ba da wannan umarnin ne bayan shugaban tsagin na jam'iyyar PDP ya kasa halartar wani zaman kotu da aka yi
- Sai dai, shugaban na PDP ya bayyana dalilin da ya hana shi zuwa zaman kotun da kuma matakin da ya dauka don ka da a cafke shi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban tsagin jam’iyyar PDP na kasa, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), ya yi martani kan umarnin cafke shi da wata kotu ta ba da.
Kabir Tanimu Turaki ya tabbatar da cewa ya ɗaukaka ƙara kan sammacin kama shi da wata babbar kotun Abuja ta bayar biyo bayan rashin halartar zaman kotun da aka tsara.

Kara karanta wannan
Turaki ya faɗa matsala: Kotu ta bada umarni a kamo shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce babban sakatarensa na musamman, Ibrahim Abdullahi, ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris 2026.
Meyasa aka umarci cafke Tanimu Turaki?
Mai shari’a Peter Kekemeke ya bayar da sammacin kama Turaki ya biyo bayan gazawarsa wajen bayyana a gaban kotun kan tuhuma guda ɗaya da ake masa.
Ana dai tuhumarsa ne kan zargin bayar da bayanan ƙarya ga shugaban ’yan sanda na kasa (IGP) a cikin wata takardar ƙara da ya rubuta a shekarar 2022.
Meyasa Turaki bai je kotu ba?
Ibrahim Abdullahi ya bayyana cewa rashin zuwan nasa ya faru ne sakamakon wata ziyarar gaggawa da ya kai asibiti.
Ya nuna cewa lauyoyinsa sun kuma shigar da buƙatar soke tuhumar, wanda a bisa ƙa’ida ba lallai ne sai ya kasance a wurin ba.
“An ba da sammacin ne saboda rashin halartar sa a kotu a yau lokacin da aka kira ƙarar. An rubuta takardar ƙarar ne a shekarar 2022, kuma saboda ziyarar asibiti ta gaggawa, ya kasa halarta."
"Bugu da ƙari, lauyoyinsa sun shigar da buƙatar neman soke tuhumar, wanda yawanci ba ya buƙatar kasancewarsa wajen shari'ar."
- Ibrahim Abdullahi

Source: Facebook
Turaki ya daukaka kara a kotu
Tawagar lauyoyin Turaki ta gaggauta shigar da ƙara tare da buƙatar dakatar da aiwatar da sammacin kama shi.
Ya jaddada cewa lamarin ba shi da alaƙa da jam’iyyar PDP amma ya nuna alamun yiwuwar akwai bita da kullin siyasa daga waje.
“Yayin da yake da muhimmanci a jaddada cewa wannan lamari ba shi da alaƙa ko kaɗan da jam’iyyar, ba za a iya kawar da yiwuwar bita da kullin siyasa daga waje ba."
- Ibrahim Abdullahi
Shugaban PDP ya koma jam'iyyar APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Zamfara ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Dr. Jamil Magayaki wanda ya shugabanci PDP ya bi sahun wasu manyan ‘yan siyasa a jihar Zamfara wajen komawa APC.
A wata sanarwa da Dr. Jamil Magayaki ya fitar, ya tabbatar da cewa ya yanke shawarar ficewa daga PDP tare da komawa APC, yana mai bayyana cewa wannan mataki ya dace da yanayin siyasar da ake ciki yanzu a jihar.
Asali: Legit.ng
