Dan Majalisar Tarayya a PDP Ya Hakura, Ya bi Sahun Masu Sauya Sheka
- Dan majalisar wakilai Abdussamad Dasuki na Kebbe/Tambuwal a jihar Sokoto ya yi murabus daga jam’iyyar PDP
- Ya sanar da komawarsa jam’iyyar ADC da ke kokarin karbe mulki a hannun APC a Najeriya a zaben shekarar 2027 mai zuwa
- Ya ce matakin sauya shekarsa ya biyo bayan tuntuba da magoya bayansa kan yadda goben siyasarsa za ta kasance
Jihar Sokoto - Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kebbe/Tambuwal a jihar Sokoto, Abdussamad Dasuki, ya yi murabus daga jam’iyyar PDP, inda ya sanar da komawarsa jam’iyyar ADC.
Dasuki ya bayyana hakan ne a cikin wata wasikar murabus da ya aike wa shugabannin jam’iyyar a matakin mazaba, inda ya ce matakin ya fara aiki nan take.
Ya ce ya dauki wannan shawara ne bayan tuntuba da abokai, magoya baya da masu ruwa da tsaki a siyasance.

Source: Twitter
Sakon da ya aikawa jam’iyyar PDP
Dan majalisar ya gode wa jam’iyyar PDP bisa damar da ta ba shi na yin siyasa da kuma wakiltar jama’a a karkashinta tsawon lokaci.

Kara karanta wannan
Hadimin Osinbajo ya raba wa ADC gardama, ya fadi mutum 2 da suka dace da yin takara a 2027
Sai dai ya bayyana cewa yanzu ya yanke shawarar ci gaba da harkokin siyasarsa a karkashin jam’iyyar ADC, inda yake ganin zai samu damar ci gaba da hidima ga al’umma.
Matakin na Dasuki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun sauyin jam’iyya daga PDP zuwa wasu jam’iyyun siyasa a sassan Najeriya.
PDP na kusan rasa masu rike da mukamai a karkashinta
Idan baku manta ba, kusan dukkan gwamnonin da aka zaba a jam’iyyar PDP sun yi murabus zuwa jam’iyyar APC mai mulki a matakin kasa.
Wannan yunkuri da gwamnoni ke yi ya jawo cece-kuce a siyasar Najeriya, inda ake yiwa gwamnatin Bola Tinubu zargin kokarin mai da Najeriya kasa mai siyasa a karkashin jam’iyyar siyasa daya.
A kwanakin baya, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, lamarin da ya jefa magoya bayansa da wadanda ke bin Kwankwaso cikin damuwa.
APC a idon duniya
A wata tattaunawa da Mehdi Hassan, dan jaridar Al-Jazeera ya yi da mai magana yawun Tinubu, Daniel Bwala, ya yi masa tambaya kan yunkurin APC na mai da Najeriya kasa mai siyasa a turbar jam’iyya daya.
Wannan na nuni da cewa, gwamnatin Najeriya na bakin duniya a wannan tsari na lallabo ‘yan adawa zuwa cikinta.
Sai dai, jam’iyya, ‘yan cikinta da makusanta shugaban kasar sun sha karyata wannan zargi tare da kare muradin tafiyar siyasar Tinubu.
Gwamna Bala na Shirin komawa APC
A wani labarin, bincike ya nuna cewa jam'iyyar adawa ta PDP na iya fuskantar rugujewa baki ɗaya, sakamakon kammala shirin Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi na komawa jam'iyyar APC a wannan makon.
Bala Mohammed, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin PDP, ya gana da Shugaba Bola Tinubu da shugabannin APC inda ya bayyana aniyarsa ta shiga jam'iyya mai mulki a ƙasa.
Duk da cewa har yanzu ana tattaunawa kan sharuɗɗan sauya shekarar, amma majiyoyi sun bayyana wa Arise News cewa an yi masa alkawarin tikitin takarar Sanata.
Asali: Legit.ng
