Kuje: Hukumar Zabe Ta Sanar da Sakamakon Zaben Ƙananan Hukumomi a Abuja

Kuje: Hukumar Zabe Ta Sanar da Sakamakon Zaben Ƙananan Hukumomi a Abuja

  • Jam’iyyar APC ta lashe kujerar shugabancin Kuje a zaben kananan hukumomin Abuja da hukumar INEC ta yi a jiya Asabar
  • Hukumar INEC ta tabbatar da cewa Danjuma Shekwolo na APC ya samu kuri’u 17,269, ya doke jam'iyyar PDP da APGA
  • Baturiyar zabe, Farfesa Nkiruka Odoh, ta sanar da cewa Shekwolo ya cika sharuddan doka kuma an tabbatar da nasararsa a zaben

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar da sakamakon zaben ƙananan hukumomi a Abuja.

Jam’iyyar APC ta lashe zaben shugabancin Kuje a zaben kananan hukumomin Babban Birnin Tarayya, Abuja.

An sanar da sakamakon zaben da aka yi a Abuja
Shugaban hukumar INEC a Najeriya, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Facebook

An sanar da sakamakon zaben Kuje

Dan takararta, Danjuma Shekwolo, ne ya zama zakara bayan samun kuri’u 17,269 a sakamakon da aka sanar a hukumance, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan zabukan Kano da Abuja, ya kira sunan Wike musamman

Da take bayyana sakamakon, baturen zabe Farfesa Nkiruka Odoh daga Jami’ar Abuja ta ce Shekwolo, bayan ya samu mafi yawan kuri’u kuma ya cika dukkan sharuddan doka, an zabe shi kuma an ayyana shi a matsayin shugaban Kuje.

Dan takarar jam’iyyar PDP, Zakwoyi Danlami, ya samu kuri’u 15,824, yayin da dan takarar APGA Abdullahi Galadima, ya samu kuri’u 4,305 a zaben.

Sakamakon Kuje ya kammala sanar da wadanda suka yi nasara a kujerun shugabanci a dukkanin kananan hukumomi shida na Babban Birnin Tarayya, kamar yadda aka tabbatar a hukumance.

Tun da farko, an ruwaito cewa Joshua Ishaku na APC ya lashe zaben shugabancin Bwari bayan samun kuri’u 18,466 a sakamakon da aka tattara.

An samu sakamakon zaben Gwahwalada a Abuja
Taswirar Abuja da aka gudanar da zaben kananan hukumomi. Hoto: Legit.
Source: Original

PDP ta lashe kujera a Gwagwalada

A Gwagwalada, dan takarar PDP, Mohammed Kasim, ya yi nasara da kuri’u 22,165, inda ya doke Yahaya Shehu na APC wanda ya samu kuri’u 17,788.

A Abaji kuwa, Umar Abdullahi Abubakar na APC ya yi nasara da kuri’u 15,536, yayin da PDP ta samu kuri’u 4,547 a sakamakon da aka sanar, cewar Premium Times.

Haka nan a Kwali, dan takarar APC, Nuhu Daniel, ya lashe zabe da kuri’u 17,032, inda ya doke Haruna Pai na PDP wanda ya samu kuri’u 8,575.

Kara karanta wannan

An buga ta: INEC ta sanar da sakamakon zaben karamar hukumar birnin Abuja

Sai dai wakilin APC, Haruna Jatau, ya nuna adawa da wasu sakamakon rumfunan zabe biyu a mazabar Gudun Karya, yana zargin an samu sabawa ka’ida.

Ya ce a kauyen Zagabutu, adadin masu kada kuri’a ya wuce na wadanda aka tantance, yayin da a Huni aka yi tantancewa da hannu maimakon amfani da na’urar BVAS.

Amma jami’in tattara sakamako, Zubairu Mohammed, ya musanta zargin, yana cewa an yi amfani da BVAS wajen tantance masu kada kuri’a a dukkan mazabar.

AMAC: APC ta lashe kujerar ciyaman a Abuja

An ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC na ci gaba da sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi da ake yi a Abuja.

Hukumar ta ayyana Christopher Maikalangu na APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban karamar hukumar birnin Abuja.

Wakilan jam’iyyu sun yaba da sahihancin tattara sakamakon, suna cewa hakan alama ce ta shirin APC na shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com