'Mulki Mafi Muni,' Hakeem Baba Ahmed Ya Yi Gargadi kan Tazarcen Tinubu a 2027
- Tsohon hadimi a fadar shugaban kasa, Hakeem Baba-Ahmed ya yi tsokaci game da tazarcen shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027 mai zuwa
- A wata hira da aka yi da shi, Dr Baba-Ahmed ya yi hasashen cewa akwai hadari mai girma a idan shugaban ya samu damar yin wa'adi na biyu a 2027
- Ya bayyana haka ne inda ya ce har yanzu bai ga wani sauyi mai ma'ana da gwamnatin Bola Tinubu ta kawo ba tun bayan ajiye aiki da ita da ya yi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon hadimi a fadar shugaban kasa kan harkokin siyasa, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa Bola Tinubu zai kasance mafi muni cikin shugabanni idan ya sake komawa mulki a shekarar 2027.
Dattijon ya bayyana haka ne yayin da 'yan siyasa ke kara shiri kan 2027 bayan hukumar INEC ta fitar da jadawalin zaben shugaban kasa da gwamnoni.

Source: Facebook
Baba-Ahmed ya yi wannan furuci ne yayin wata hira da tashar Channels Television a cikin shirin siyasa a ranar Talata, 17 ga Fabarairun 2026.
Batun cigaba da mulkin Bola Tinubu
Hakeem Baba-Ahmed ya ce bai ga wani sauyi mai ma’ana ba a shugabancin Tinubu tun bayan murabus ɗinsa daga muƙamin mai ba da shawara, maimakon haka ya ce abubuwa sun ƙara taɓarɓarewa.
Ya ce:
“Ƙasarmu ta fi fuskantar matsalar tsaro yanzu fiye da lokacin da na bar aiki. Abin da nake gani a gida da kuma kan tituna yayin da mutane ke magana shi ne tsananin ƙunci da talauci, musamman a Arewacin ƙasar nan.
Yayin da ya ke sharhi kan wadanda suka kewaye Tinubu, Hakeem Baba-Ahmed ya ce:
“Ina ganin shugaban ƙasa yana tara ’yan siyasa a kusa da shi da fatan cewa su ne za su taimaka masa ya samu wa’adi na biyu.
“Wannan tunani ne maras kyau. Ba dabara ba ce, kuma ba irin Tinubu ba ne da muka saba ji ana magana a kansa.
Gargadi kan tazarcen Tinubu a 2027
Rahoton jaridar the Sun ya nuna cewa Dr Hakeem Baba-Ahmed ya yi hasashen cewa idan shugaba Bola Tinubu ya zarce zai zama shugaba mafi muni a tarihin Najeriya.
Ya ce:
“Ina ganin shugaba Tinubu zai zama mafi muni cikin shugabanni idan ya dawo kan mulki a 2027,”

Source: Facebook
Dr Hakeem ya yi aiki a fadar shugaban kasa a ofishin mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima kafin ya yi murabus a Afrilun 2025.
Amurka: Bukarti ya aika wa Tinubu tambayoyi
A wani labarin, kun ji cewa lauya mai fashin baki, Audu Bulama Bukarti ya aika da tambayoyi ga shugaba Bola Tinubu kan jibge sojojin Amurka a Bauchi.
Bulama Bukarti ya ce akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta fada wa 'yan kasa yaushe sojojin Amurka za su tafi, a ina za su yi aiki da kuma irin aikin da za su yi.
Lauyan ya kara da tambayar dalilin kai sojojin jihar Bauchi maimakon wasu jihohin da ake yaki da 'yan ta'adda kamar Zamfara, Niger da Borno.
Asali: Legit.ng

