Sanatocin da Za Su Nemi Ajiye Aikin Majalisa Su Yi Takarar Gwamna a Zaben 2027
FCT, Abuja - Duk da cewa akwai sauran lokaci kafin zuwan 2027, manyan ’yan siyasa sun riga sun fara shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar.
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Akwai sanatocin da za su nemi takarar gwamna a jihohinsu a zaben da za a yi a shekarar 2027 da ake tunkara.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro sanatocin da ake ganin za su nemi takarar gwamna a jihohinsu a zaben 2027.
Sanatoci na harin kujerar gwamna a 2027
Wasu daga cikin sanatocin sun fito sun ayyana aniyarsu ta fitowa takara a zaben domin jagorantar jihohinsu.
Hakazalika, akwai wadanda kuma wasu kungiyoyi ke kiraye-kirayen su fito takarar gwamna a 2027 duk da su ba su ayyana burin rike mulkin jihohinsu ba.
Yayin da shirye-shirye ke karuwa, akwai alamun cewa ƙarin mambobin majalisar dattawa za su shiga takarar gwamna a jihohinsu, sakamakon yadda ake samun haɗaka da sake lale a kullum.
1. Ahmad Lawan (Yobe)
Ana hasashen cewa Sanata Ahmad Lawan zai fito takarar gwamnan jihar Yobe a zaben shekarar 2027.

Source: Facebook
Sanata Ahmad Lawan, wanda yake wakiltar mazaɓar Yobe ta Arewa tun shekarar 2007, ya yi shugaban majalisar dattawa daga 2019 zuwa 2023.
Jaridar Daily Trust ta ce wasu mambobin jam’iyyar APC a jihar Yobe sun bukaci Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, da ya tsaya takarar gwamnan jihar Yobe a zaɓen 2027.
Matasan a karkashin inuwar ‘Daga Buni sai Bade’ (ma’ana bayan Gwamna Mai Mala Buni, sai Ahmad Lawan) sun yi wannan kiran ne a garin Potiskum.
A cewarsu, sun amince da Sanata Ahmad Lawan ne saboda tarihin ayyukansa ga jihar da ma kasa baki ɗaya.
Duk da ilmin zamani, kwarewa da sanin aikinsa, masu bibiyar siyasar Yobe suna ganin zai iya fuskantar kalubalen zama gwamna saboda mutanensa ba su da rinjaye a jihar.
2. Abdulfatai Buhari (Oyo)
Abdulfatai Buhari, sanata mai wakiltar Oyo ta Arewa, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Oyo.

Source: Facebook
Jaridar Daily Post ta ce a wata hira da ya yi da manema labarai, babban jigon na APC ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Oyo.
“Na riga na bayyana cewa ba na sha’awar sake neman kujerar Sanata, domin ni ma ina so na gwada sa’ata a takarar gwamna. Ba wai na damu da hakan ba ne; na bar wa Allah komai.
- Abdulfatai Buhari
Idan ya samu takara a jam'iyyar APC, sanatan zai dage wajen ganin ya ga bayan PDP da gwamnanta Seyi Makinde zai bar ofis a Mayun badi.
3. Mohammed Onawo (Nasarawa)
Wani sanatan da ake kyautata zaton yana da niyyar takarar gwamnan jihar Nasarawa shi ne Sanata Mohammed Onawo, mai wakiltar mazaɓar Nasarawa ta Kudu.

Source: Facebook
Sai dai har yanzu burin nasa yana matsayin jita-jita ne tunda bai riga ya sanar da hakan ba.
Idan Onawo ya nemi samun tikiri, ana ganin zai buga da wasu abokan aikinsa da kuma tsohon Sufetan 'ayan sandan Najeriya, Mohammad Adamu.
4. Aliyu Wadada (Nasarawa)
Sanata Ahmed Wadada ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Nasarawa a zaben 2027.

Source: Facebook
A kwanakin baya ya fito ya musanta rahoton da ke yawo na cewa ya janye daga takarar gwamnan jihar Nasarawa kwanaki bayan barin jam'iyyar adawa zuwa APC.
Jaridar The Punch ta ce a cikin wata sanarwa da babban mataimakinsa, Sam Israel ya fitar, ya siffanta rahoton janyewar Wadada a matsayin "tsabagen karya" wanda wasu ’yan siyasa waɗanda farin jinin sanatan ke tsorata su suka kirkira domin yaudarar jama'a.
5. Sharafadeen Alli (Oyo)
Ana hasashen sanata mai wakiltar Oyo ta Kudu, Sharafadeen Alli, zai fito takarar gwamnan jihar Oyo.

Source: Facebook
Shafin The Hope Newspaper ya ce Sanata Sharafadeen Ali wanda tsohon sakataren gwamnatin jiha (SSG) ne, yana shirin tsayawa takarar gwamna a karkashin inuwar APC.
6. Tahir Monguno (Borno)
Ana hasashen Sanata Mohammed Tahir Monguno da ke wakiltar Borno Arewa, zai hakura da majalisa ya nemi takarar gwamnan Borno.

Source: Facebook
Sanata Mohammed Monguno shi ne babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa ta 10 kuma tsohon babban lauyan gwamnati na jihar Borno.
Masu sha'awar ya gaji Babagana Zulum suna ganin ya kamata gwamna ya bar tsakiyar Borno a 2027.
7. Shehu Buba (Bauchi)
Sanata Shehu Umar Buba na daga cikin 'yan siyasa da ake hasashen za su fito takarar gwamnan jihar Bauchi.

Source: Facebook
Jaridar PR Nigeria ta ce wata gagarumar haɗaka ta mazaɓar Bauchi ta Kudu, karkashin inuwar ƙungiyar Shehu Buba Organisation (SBO), ta gabatar da bukatarta ga jam’iyyar APC ta jihar Bauchi, kan Sanata Shehu Umar Buba.
Kungiyar ta yi kira ga jam’iyyar APC da ta lallashi Sanata Shehu Buba Umar domin ya tsaya takarar gwamna a zaɓen shekarar 2027.
Kamar a Oyo, Kwara da Borno, shi ma gwamnan Bauchi zai bar ofis a 2027 don haka yake neman yana da ta-cewa game da wanda zai gaje ji.

Kara karanta wannan
Ramadan na karatowa, za a yi gyaran iskar gas da zai rage wutar lantarki a Najeriya
8. Saliu Mustapha (Kwara)
Sanata Saliu Mustapha na da burin fitowa takarar gwamnan jihar Kwara a karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Source: Facebook
Burin takarar sanatan ta sanya ana zaman doya da manja tsakaninsa da Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq.
9. Lola Ashiru (Kwara)
Sanata Lola Ashiru ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Kwara a zaben shekarar 2027.

Source: Facebook
Jaridar Premium ta ce sanatan ya bayyana cewa ya yanke wannan shawara ne saboda zai iya kawo ci gaba ga jihar Kwara.
10. Abdul Ningi (Bauchi)
Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya na daga cikin masu sha’awar tsayawa takarar gwamnan jihar Bauchi.

Source: UGC
Jaridar TheCable ta ce jigon na jam'iyyar PDP na iya hakura da majalisa domin neman zama magajin Gwamna Bala Mohammed a 2027.
A lokacin da ake ganin bai tare da gwamna Bala Mohammed, wasu sun ce Abdul Ningi yana cikin na hannun daman Atiku Aubakar.
Majalisa ta sauya matsaya kan dokar zabe
A wani labarin kuma, kun ji cewa Majalisar dattawa ta sauya matsaya kan tura sakamakon zabe ta yanar gizo.
Majalisar dattawan ta janye matsayar da ta cimma a baya na kin amincewa da tura sakamakon zabe kai-tsaye daga rumfunan zabe zuwa shafin adana bayanan sakamako na hukumar INEC watau (IReV).
Mafi akasarin sanatocin sun kada kuri’ar amincewa da sabon gyaran lokacin da aka gabatar da batun domin kada kuri’a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng




