Atiku Ya Samu Abokin Takara don Fafatawa a Zaben 2027? An Ji Yadda Lamarin Yake

Atiku Ya Samu Abokin Takara don Fafatawa a Zaben 2027? An Ji Yadda Lamarin Yake

  • Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Peter Ayodele Fayose, ya bayyana cewa Gwamna Seyi Makinde ya cimma yarjejeniya da Atiku Abubakar don zaben 2027
  • Atiku Abuakar ya fito ya yi martani kan kalaman na Fayose masu nuna cewa Makinde zai zama mataimakinsa don zaben shekarar 2027
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa Fayose ya saba yada gutsiri tsoma da gulmar siyasa

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi martani kan kalaman tsohon gwamnan jihar Ekiti, Peter Ayodele Fayose.

Atiku ya bayyana Fayose a matsayin "shahararren mai gulmar siyasa," inda ya bukaci jama'a da su yi watsi maganganun da ya yi game da batun tikitin mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ADC.

Atiku ya karyata kalaman Fayose
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa ga jama'a, Phrank Shaibu, ya fitar a shafin X a ranar Alhamis, 12 ga watan Fabrairun 2027.

Kara karanta wannan

Bayan samun mukami, tsohon mai sukar Tinubu ya fadi abin da zai sa ya zarce a 2027

Fayose ya yi ikirarin cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince zai tsaya takarar mataimakin shugaban kasa tare da Atiku a zaben 2027 mai zuwa, tare da alkawarin bayar da gudunmawar Naira biliyan 10.

Wane martani Atiku ya yi?

Atiku ya bayyana cewa ba a taba yin wata tattaunawa kan batun tikitin mataimakin shugaban kasa na ADC ba yayin ziyarar da ya kai gidan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida (mai ritaya) kwanan nan.

Fayose ya yi ikirarin cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince zai tsaya takarar mataimakin shugaban kasa tare da Atiku a zaben 2027 mai zuwa, tare da alkawarin bayar da gudunmawar Naira biliyan 10.

Phrank Shaibu ya ce babu wani lokaci da Atiku Abubakar ya taba shiga wata yarjejeniyar siyasa ta bogi kamar yadda aka siffanta a cikin rubutun na Fayose.

Atiku ya karyata Fayose

A cewar Shaibu, labarin na Fayose ba bayanan sirri ba ne na cikin gida, kirkirarren labari ne wanda aka tsara domin yaudarar mutane, dauke hankali, da kuma tunzura su.

"Bari mu fito mu bayyana karara cewa, dukkan wannan rubutu tulin karya ne tsantsa, karyar da shahararren mai yada gulmar siyasa ya hada, wanda abin da kawai ya rage a kimarsa shi ne kawai tayar da cece-kuce, murdiya, da farfaganda mai arha."

Kara karanta wannan

Fayode ya fallasa yadda zaman Atiku da Makinde ya kaya a gidan Janar IBB

"Ba a yi tattaunawa kan tikitin mataimakin shugaban kasa ba. Ba a yi tattaunawa kan gudunmawar Naira biliyan 10 ba."
"Ba a yi magana kan tsarin karba-karba ba. Ba a ba da tabbacin kawo kuri'un deligets ba. Kuma babu wani 'taron Dubai' na sirri da aka tsara kan wannan batun."
"Harkokin siyasar mai girma Atiku Abubakar suna ginuwa ne a kan manyan ka'idoji na kasa, ba irin wasan kwaikwayon na neman kudi da aka kera a cikin wancan rubutun ba."
"Abin takaici ne yadda wasu mutane, wadanda suka dade da rasa kima a siyasa, yanzu suke kokarin neman suna ta hanyar tsara tatsuniyoyi kan manyan mutane. Karya na iya yin tasiri na dan lokaci, amma tana rugujewa a gaban gaskiya."
"Atiku Abubakar ba ya siyasa a boye, ko ta hanyar cin hanci, ko ta hanyar matsananciyar damuwa ta neman mulki kamar yadda aka siffanta shi cikin rashin mutunci."
"Ya ci gaba da mayar da hankali kan tattaunawa mai ginuwa kan ka'ida da neman ceto kasa, ba wasan kwaikwayon bayan fage da masu neman suna suka tsara ba."

Kara karanta wannan

Shekarau: Yayan tsohon gwamnan Kano ya riga mu gidan gaskiya bayan jinya

- Phrank Shaibu

Atiku ya musanta kalaman Fayose
Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Hoto: @atiku
Source: Facebook

Sanarwar ta shawarci jama'a da su kalli bayanan na Fayose da idon raini domin abin da ya dace da shi ke nan.

Atiku ya yi zargi kan majalisar dattawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi zargi kan majalisar dattawa.

Atiku Abubakar ya ce majalisar dattawa ta shimfida hanya domin magudin babban zaben shekarar 2027 ta hanyar jinkirta gyaran dokar zabe ta 2022.

Ya bayyana cewa idan ana son gyara kura-kuran da aka gani a zaben 2023, dole ne a gaggauta sake duba tsarin doka da ke tafiyar da zabe kafin a kai ga shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng