'Dan Majalisar Wakilai daga Kano na Tsaka Mai Wuya, NNPP na Neman Raba Shi da Mukaminsa

'Dan Majalisar Wakilai daga Kano na Tsaka Mai Wuya, NNPP na Neman Raba Shi da Mukaminsa

  • Jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano ta zargi mamba mai wakiltar Dala a Majalisar wakilai, Hon. Aliyu Sani Madakin Gini da cin amanarta
  • NNPP ta bukaci Majalisar wakilai ta sauke Madaki daga matsayin Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye, tare da maye gurbinsa da wani
  • Mai magana da yawun NNPP na Kano, Ibrahim Karaye ya ce Madaki ya halarci taron APC a Dala, wanda hakan ya sabawa dokar jam'iyya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - 'Dan Majalisar wakilan tarayya daga jihar Kano, Hon. Aliyu Sani Madaki ya fara fuskantar matsala daga jam'iyyarsa ta NNPP.

Hakan dai ya biyo bayan zargin da jam'iyyar NNPP reshen Kano ta masa cewa yana yi mata zagon kasa tare da shiga wasu ayyuka cin amanar jam'iyya.

Hon. Aliyu Sani Madaki.
Mataimakin shugaban mai tsawatarwa na jam'iyyun adawa a Majalisar Wakilai, Hon. Aliyu Sani Madaki Hoto: Aliyu Sani Madaki
Source: Facebook

NNPP ta nemi a cire Hon. Aliyu Madaki

Kara karanta wannan

Kwankwaso: NNPP ta yi martani mai zafi da Amurka ta kawo batun kakaba wa jagoranta takunkumi

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa NNPP reshen jihar Kano ta bukaci a cire dan Majalisar daga matsayin mataimakin shugaban marasa tinjaye a Majalisar wakilai.

Jam’iyyar ta zargi Hon Aliyu Madaki, wanda ke wakiltar mazabar Dala ta Tarayya a Kano, da karya kundin tsarin NNPP ta hanyar halartar wasu taruka na jam'iyyun da take adawa da su.

NNPP ta zargi dan Majalisar wakilan da halartar taron ƙungiyar magoya bayan APC a ƙaramar hukumar Dala tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar, wanda hakan ya saba wa dokokinta.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na NNPP a jihar Kano, Ibrahim Karaye, ya fitar a ranar Laraba, 11 ga watan Fabrairu, 2026.

Sakon da NNPP ta tura Majalisar Wakilai

A cikin sanarwar, jam’iyyar NNPP ta bukaci majalisar wakilai ta sauke Hon. Aliyu Nadaki daga matsayin Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye nan take, cewar Daily Trust.

NNPP ta bayyana cewa ba za ta kyale wani mambanta ya ci amana ko yin wasu ayyuka da suka saba wa kundin tsarin mulkinta ba.

Jam’iyyar ta ce Madaki bai sanar da ficewarsa daga NNPP a hukumance ba, kuma bai bayyana sauya sheƙarsa zuwa wata jam’iyya ba.

Kara karanta wannan

'Tinubu ya fara yi wa godiya, ba Allah ba': Naja'atu Mohammed ta dura kan Abba Kabir

“Jam’iyyar NNPP na buƙatar Majalisar Tarayya da ta maye gurbin Hon. Aliyu Sani Madaki da wani mamba mai biyayya ga NNPP domin kare muradun jam’iyyun adawa a Majalisar, tare da hana yunƙurin APC na maida Najeriya tsarin jam'iyya daya,” in ji Karaye.
Majaliaar wakilai.
Yan Majalisa suna zama a zauren Majalisar wakilan tarayya Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, Hon. Madaki bai fito fili ya mayar da martani kan zarge-zargen ba ko kuma bukatar da jam’iyyar ta gabatar ba.

NNPP ta nesanta kanta da kalaman Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta nesanta kanta da kalaman tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

NNPP ta bayyana cewa maganganun da Kwankwaso ya yi cewa ya kai Abba Kabir zuwa wurin alkalan kotun koli a 2019, ba su da alaka sa ita domin ya yi su tun kafin ya shiga jam'iyyar.

Jam’iyyar ta buƙaci ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa (NBA) da ta goge sunan NNPP daga kowace irin takardar ƙorafe-ƙorafe da ta miƙa wa Sufeto Janar na ƴan sanda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262