Tun kafin a Yi Nisa, An Sauke Gwamna daga Matsayin Shugaban Kwamitin Taron APC na Kasa

Tun kafin a Yi Nisa, An Sauke Gwamna daga Matsayin Shugaban Kwamitin Taron APC na Kasa

  • Jam'iyyar APC ta yi garambawul a kwamitin shirya babban taron ta na kasa da ta kafa kwanakin baya, ta sauya Gwamna Hope Uzodinma
  • A gyaran da jam'iyyar ta yi, tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya zama shugaban kwamitin shirya taron
  • Jam'iyya mai mulki ta kuma fadada kwamitin daga mutum 73 zuwa 90, sannan ta maida Gwamna Imo, Hope Uzodinma daga shugaba zuwa ma'aji

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam’iyyar APC ta sauke Shugaban kungiyar gwamnoninta kuma Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma daga matsayin shugaban kwamitin shirya babban taro na kasa.

APC ta kuma sanar da maye gurbinsa da tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a matsayin sabon shugaban kwamitin da zai jagoranci shirya babban taronta na kasa.

Gwamnan Imo.
Shugaban gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma Hoto: Hope Uzodinma
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren Tsare-tsare na APC ta kasa, Surajudeen Basiru, wadda aka wallafa a shafin X na jam’iyyar ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

An yi musayar kalamai bayan rigima ta barke tsakanin APC da tsohon shugabanta na kasa

Wannan taro na jam'iyyar APC, an shirya gudanar da shi ne a ranakun 27 da 28 ga watan Maris na shekarar 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa:

“Bayan kara tuntubar shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, an sake yin gyare-gyare a Kwamitin Gudanarwa na Taron Kasa na 2026. Za a nada tare da sanar da kananan kwamitoci nan gaba kadan.”

Gyaran da APC ta yi a kwamitin taron

Gwamna Hope Uzodimma, wanda tun farko aka nada a matsayin shugaban kwamitin, yanzu an mayar da shi Ma'aji biyo bayan garambawul din da shugabannin jam'iyyar suka amince da shi.

Sai dai duk da gyaran da aka yi, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe na nan a matsayinsa na sakataren kwamitin.

Jam’iyyar APC ta kuma fadada mambobin kwamitin daga mutum 73 zuwa 90, inda aka shigo da wasu jiga-jigan jam’iyyar, ciki har da Sanata Barry Mpigi.

Yadda kwamitin shirya taron APC ya koma

Matsayi

Suna

Shugaban kwamiti

Aminu Bello Masari (Tsohon Gwamnan Katsina)

Mataimakin Shugaba I

Anyim Pius Anyim (Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa

Mataimakin Shugaba II

Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq

Sakatare

Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni

Ma'aji

Gwamnan Imo, Hope Uzodinma

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kausasa harshe kan harin 'yan ta'adda a Kwara, ya dauki mataki

Wannan garambawul na zuwa ne yayin da jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ke kara kaimi wajen ganin babban taron nata ya gudana cikin nasara a watan gobe, in ji jaridar Daily Trust.

Tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari.
Tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari a taron masu ruwa da tsakin APC Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

APC ta hango nasara a zaben 2027

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa za su samu nasara a babban zaben 2027.

Farfesa Nentawe Yilwatda ya ce jam’iyyar ADC ba ta da karfin da za ta iya kalubalantar APC gabanin zaɓen da za a yi shekarar 2027, yana mai cewa APC ba tsarar jam'iyyar hadaka ba ce.

Haka kuma, ya yi watsi da tasirin siyasa da wasu jagororin adawa ke da shi, ciki har da shugaban ADC na kasa kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262