Gwamnatin Kano: Binciken Ganduje na nan duk da Abba Ya shigo jam'iyyar APC

Gwamnatin Kano: Binciken Ganduje na nan duk da Abba Ya shigo jam'iyyar APC

  • Gwamnatin Kano ta yi magana a kan zarge-zargen cin hanci da rashawa a kan tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje
  • Kwamishinan yada labarai na Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana halin da ake ciki bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma APC
  • Ya jaddada cewa sauya sheƙar Gwamna Abba Yusuf zuwa APC ba ta shafi shari’ar ba da ake yi da tsohon gwamnan a kotunan Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Ibrahim Waiya, ya bayyana mahangar gwamnati a kan shari'o'in tsohon Shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje.

Yana wannan batu ne a bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka zuwa APC a ranar Litinin 26 ga watan Janairu, 2026, jam'iyyar da Ganduje ya zama jigo a cikinta.

Kara karanta wannan

Daga sauya sheƙar Abba, Tinubu ya amince da aikin Naira tiriliyan 1 a Kano

Gwamnatin Kano ta yo magana a kan shari'ar Ganduje
Gwamna Abba Kabir Yusuf, Tsohon Shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Sanusi Bature D-Tofa/Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Source: Facebook

A hira da ya yi da Arise News, Waiya ya ce zarge-zargen cin hanci da ake yi wa tsohon gwamnan jihar, Dakta Umar Abdullahi Ganduje, na nan daram a gaban shari’a.

Matsayar gwamnatin Kano kan shari'ar Ganduje

Daily Post ta ruwaito cewa a cewar Kwamishinan, tsarin shari’a a Najeriya ya tanadi cewa ana iya tuhumar mutum da laifuffuka da dama.

Sai dai a cewarsa, kotu ce kawai ta ke da hurumin ta tabbatar da shi a matsayin mai laifi, inda ya kara da cewa har yanzu babu wata kotu da ta tabbatar da laifin Ganduje.

Waiya ya ce Abba ya koma APC ne saboda Kanwa
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Ambasada Abdullahi Waiya ya kara da cewa:

“Matukar tsarin shari’a na Najeriya ya shafi lamarin, ana iya zargin mutum da cin hanci ko wasu laifuffuka, amma abu mafi muhimmanci shi ne idan kotu ta tabbatar da laifinsa."

Ya kara da cewa zarge-zargen cin hanci na nan a gaban tsarin shari’a, kuma gwamnati ba ta da niyyar tsoma baki ko yin katsalandan a aikin kotuna.

Kara karanta wannan

Kwamishinoni 5 da suka yi murabus a gwamnatin Abba suka bi Kwankwaso

Waiya ya ce:

“Ganduje bai taba samun hukunci daga kowace kotu da ke tabbatar da cewa ya aikata wadannan zarge-zarge ba. Babu wata kotu da ta taba ayyana shi da laifi kan irin wadannan tuhume-tuhume.”

Ana son samar da Kano sabuwa - Waiya

A cewarsa, Kano na cikin wani sabon yanayi na sauye-sauye, inda gwamnati ke kokarin hada kowa da kowa domin ci gaban jihar.

Kwamishinan ya kuma yi tsokaci kan sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Ya bayyana cewa wannan mataki ne da aka dauka domin samar wa mutanen Kano mafita da kuma habaka jihar baki daya.

Waiya ya bayyana cewa sauya sheƙa lamari ne na siyasa, amma hakan ba ya nufin zai shafi shari'ar da ake yi a kan Ganduje.

Ya jaddada cewa manufar gwamnati ita ce samar da zaman lafiya, haɗin kai da mutunta doka da kuma ci gaban Kano.

Abba: Ganduje ya maida martani ga Kwankwaso

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya kara samun karbuwa a APC awanni 24 bayan ya shiga jam'iyyar

A baya, mun wallafa cewa siyasar jihar Kano na ci gaba da ɗaukar sabon salo yayin da jam’iyyar APC, tun bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka.

Tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, da kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun bayyana mabambantan ra'ayoyi kan zaben 2027.

Tsohon gwamna Ganduje ya yi martani ga kalaman Rabiu Musa Kwankwaso da ke alamta cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ba zai kai labari a babban zaben 2027 mai zuwa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng