Bayan Gama Tarbar Abba zuwa APC, Barau Ya Tabo Batun Burinsa na Takarar Gwamna a 2027

Bayan Gama Tarbar Abba zuwa APC, Barau Ya Tabo Batun Burinsa na Takarar Gwamna a 2027

  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yi farin cikin dawowar Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano zuwa jam'iyyar APC mai mulki
  • Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa yanzu lokaci ne da za su taimaka wa gwamnan da shawarwari, addu'o'i domin ya samu nasara kan abin da ke gabansa
  • Hakazalika, mataimakin shugaban majalisar dattawan ya bayyana makomar burinsa na tsayawa takarar Gwamnan Kano a zaben shekarar 2027 da ake tunkara

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi wa Gwamna Kabir Yusuf maraba zuwa jam'iyyar APC.

Sanata Barau ya kuma bayyana cewa ya hakura da takarar gwamnan Kano a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Sanata Barau ya yi farin cikin dawowar Abba zuwa APC
Sanata Barau Jibrin na kus-kus da Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen taron dawowarsa APC Hoto: Barau I Jibrin
Source: Facebook

Sanata Barau ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai wadda ya sanya a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 27 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Abin da Kwankwaso da mutanen Kano suka dauki hadewar Gwamna Abba da Ganduje a APC

An yi tattaunawar ne bayan tarbar Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda ya sake komawa jam'iyyar APC.

Barau ya yi murna kan dawowar Abba APC

Sanata Barau ya bayyana cewa ya yi farin ciki kan dawowar gwamnan zuwa APC, domin jam'iyyar ta samu karuwa.

"Rana ce wadda zan kwana da farin ciki saboda jam'iyyata ta samu karuwa. Karuwar watau gwamna sukutum."
"Idan ba a manta ba kullum da na fi shekara ina karbar 'yan jam'iyyu daban-daban ciki har da 'yan jam'iyyar NNPP. Sai ga shi yau Allah da ikonsa gwamnan Kano ya shiga jam'iyyarmu. Saboda haka muna godewa Allah kan wannan karuwa da muka samu."
"Babban abin da ke gabanmu shi ne mu ba shi hadin kai, mu taimaka masa ta hanyar ba shi shawarwari da addu'o'i don ya samu nasara."

- Sanata Barau Jibrin

Batun takarar Barau a zaben 2027

Sanata Barau Jibrin ya kuma bayyana cewa ya hakura da batun takarar gwamnan Kano a zaben 2027.

Barau ya ce ya hakura da takarar gwamna a zaben 2027
Sanata Barau Jibrin tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen komawa APC Hoto: Barau I Jibrin
Source: Facebook
"Babu wannan, dalili saboda shi ne har idan kishin al'umma muke, idan muka ce to ga gwamna nan, don jam'iyyarmu, na farko hadin kai muke son mu ba shi ya yi aiki, don ya samu kwanciyar hankali da sukuni."

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Gwamna Abba ya shiga jam'iyyar APC a gaban Ganduje da Barau

"Idan kuma ba ka tabbatar masa da cewa za ka kyale shi za ka bar shi ya sake yin wani zangon ba, ka sanya shi a cikin tararrabi da kuma tunanin wai shin zan samu zarcewa, zai shafi kokarin da yake yi, zai shafi aikinsa."

- Sanata Barau Jibrin

Ganduje ya ayyana jagoran APC a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya tarbi Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano zuwa jam'iyyar.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa bisa al’adar jam’iyyar APC, Gwamna Abba Kabir Yusuf zai zama jagoran jam’iyyar a jihar Kano kai tsaye.

Ganduje ya kuma tabbatar wa gwamnan cewa za a yi masa adalci a cikin jam’iyyar, yana mai nuna kwarin gwiwar cewa APC za ta samu gagarumar nasara a zabubbuka masu zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng