Zance Ya Kare; Gwamna Abba Na Kano Ya Fice daga Jam'iyyar NNPP
- Jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya ta rasa gwamna daya tilo da take da shi daga cikin a jihohi 36 na kasar nan
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da murabus dinsa daga jam'iyyar NNPP wadda ya lashe zabe karkashinta a shekarar 2023
- Abba Kabir Yusuf ya yi bayani kan dalilin da ya sanya ya yanke shawarar raba gari da jam'iyyar NNPP wadda ya kasance a cikinta tun shekarar 2022
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya aike da takardar murabus daga jam’iyyar NNPP a hukumance.
Gwamna Abba ya danganta matakin da ya dauka da rikice-rikicen cikin gida da rikicin shugabanci da ke kara ta’azzara a jam’iyyar.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a, 23 ga watan Janairun 2026.
Gwamna Abba ya raba gari da NNPP
A cewar sanarwar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da murabus dinsa ne ta cikin wata wasika da ya aikawa shugaban NNPP na mazabar Diso-Chiranchi, da ke karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.
Sanarwar ta kara da cewa murabus din zai fara aiki ne daga ranar 25 ga Janairu, 2026, bayan da gwamnan ya nuna damuwa kan yadda rikice-rikice ke ci gaba da girgiza jam’iyyar.
Meyasa Gwamna Abba ya bar NNPP?
A cikin wasikar da ya rubuta, gwamnan ya ce ya yi hakan ne cike da godiya, inda ya sanar da shugabancin NNPP a hukumance game da matakinsa na yin murabus daga zama mamban jam’iyyar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna godiyarsa ga jam’iyyar bisa ba shi damar tsayawa takara, tare da irin goyon baya da ya samu daga shugabanni da mambobin jam’iyyar a fadin jihar Kano.
“Har yanzu ina matukar yin godiya kan damar da jam’iyyar, shugabancinta da mambobinta a fadin jihar Kano suka ba ni na kasancewa cikin tafiyarta ta siyasa tun daga shekarar 2022, da kuma goyon baya, fatan alheri da hadin kai da aka nuna mini a lokacin da nake cikin jam’iyyar."
- Gwamna Abba Kabir Yusuf

Source: Facebook
Sai dai gwamnan ya danganta matakinsa da abin da ya kira rikice-rikicen cikin gida da ba a warware ba, tare da tsawaitattun shari’o’i da suka ci gaba da girgiza tsarin jam’iyyar a matakin jiha da kasa baki daya.
“A ‘yan kwanakin nan, jam’iyyar ta fuskanci matsaloli masu ta’azzara a cikinta sakamakon sabanin shugabanci da kuma shari’o’in da ke gudana, da dama daga cikinsu suna gaban kotuna domin yanke hukunci."
- Gwamna Abba Kabir Yusuf
Ya kara da cewa wadannan rikice-rikicen sun jawo karuwar rashin jituwa tsakanin mambobin jam’iyyar, wanda ya haddasa rarrabuwar kai da kuma raunana hadin kai.
Wadanda suka bar NNPP tare da Abba
A halin da ake ciki kuma, sanarwar ta bayyana cewa murabus din gwamnan ya zo ne tare da na ‘yan majalisar dokokin jihar Kano 21.
Sauran wadanda suka yi murabus sum hada da 'yan majalisar wakilai takwas, da kuma shugabannin kananan hukumomi 44 a fadin jihar Kano.
Gwamna Abba ya kafa tawaga
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na ci gaba da shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.
Abba Kabir Yusuf ya amince da kafa wata tawaga ta musamman domin sanar da jagoran NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, game da shirin sauyin sheka zuwa APC.
Wata majiya ta bayyana cewa Gwamnan ya amince cewa, bisa ladabi da girmamawa, ya dace a sanar da Kwankwaso a hukumance kafin a bayyana sauyin shekar.
Asali: Legit.ng


