Bayan Ganawa da Tinubu, An Kara Zuga Gwamna Abba kan Rabuwa da Kwankwaso
- Batun sauya shekar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf zuwa APC na ci gaba da jan hankali bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu
- Alhaji Liadi Tella ya shawarci Gwamma Abba ya shiga APC ko da kuwa ubangidansa kuma jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso bai yarda ba
- Jigon APC ya ce sauya shekar gwamnan zai ba shi damar tsayawa da kafarsa, kuma ya samu taimakon gwamnatin tarayya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Wani jigo a APC, Alhaji Liadi Tella ya tsoma baki a siyasar Kano bayan ganawar da aka yi jiya tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
'Dan siyasar ya bukaci gwamnan Kano da ya dauki "mataki na jarumtaka da dabara" ta hanyar komawa APC, ko da kuwa ubangidansa na siyasa, Rabiu Musa Kwankwaso bai amince ba.

Source: Facebook
An kara zuga Abba ya bar Kwankwaso
Yayin da yake zantawa da jaridar The Guardian, Liadi ya bayyana cewa tafiya tare da APC da Shugaba Tinubu zai ba wa Gwamna Abba damar samun karfin fada a ji fiye da ya ci gaba da zama karkashin inuwar Kwankwaso.
“Idan Gwamna Abba ya ci gaba da zama karkashin ikon Kwankwaso har zuwa 2027, babu makawa sai abu guda ya faru, ba zai samu tikitin takara ba a karkashin NNPP.
“Saboda haka komawa APC ba dabarar siyasa ba ce kawai, zai kuma tabbatar masa da cin gashin kansa, zai zama jagoran jam’iyya a Kano, ba tare da takura daga kowane ubangidan siyasa ba.”
Yadda rikici ya turnike Kwankwasiyya
Abba, wanda tsohon kwamishina ne a karkashin Kwankwaso, ya lashe zaben gwamnan Kano a 2023 da taimakon Kwankwasiyya da NNPP, wanda hakan ya kawo karshen mulkin APC na shekaru takwas a Kano.
Tun bayan hawansa mulki, masu sharhi kan al’amuran siyasa sun lura da rikicin da ke tasowa tsakanin Abba da ubangidansa, musamman kan batun nade-nade, tsara manufofin gwamnati, da iko da jam’iyya, in ji rahoton The Nation.
Wadannan matsaloli sun kara rura wutar jita-jitar sauya shekar gwamnan Kano, musamman yayin da APC ke kara kaimi wajen ganin ta kwace Kano a zaben 2027.
Liadi Tella ya nanata cewa shiga APC zai ba gwamnan ikon gudanar da mulkin Kano tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya ba tare da tsangwama ba.

Source: Facebook
Tinubu da APC na bukatar Kwankwaso?
Game da tasiri karfin siyasar Kwankwaso kuwa, Liadi ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan Kano ya fara rasa kima da farin jininsa a matakin kasa.
Ya ce:
“Ba na jin Shugaba Tinubu ko APC na bukatar Kwankwaso kafin su yi nasara a Kano a 2027, idan aka yi la’akari da yanayin siyasar jihar a halin yanzu.”
Tinubu ya sharewa Abba hanyar shiga APC
A wani labarin, kun ji cewa bayanai sun nuna cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shirya sauya sheka daga NNPP zuwa APC bayan ganawarsa da Shugaba Tinubu.
Majiyoyi da dama da ke da masaniya kan ganawar sun bayyana tattaunawar ta warware muhimman matsalolin da suka jawo jinkirin komawar Abba APC.
Majiyoyi sun ce shugaban kasa ya tabbatar wa Abba Gida-Gida da kansa cewa za a daraja shi a APC, musamman a Kano da kuma yankin Arewa maso Yamma.
Asali: Legit.ng


