Wike Ya Maida Martani ga Masu Bukatar Tinubu Ya Tsige Shi daga Kujerar Ministan Abuja

Wike Ya Maida Martani ga Masu Bukatar Tinubu Ya Tsige Shi daga Kujerar Ministan Abuja

  • Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wile ya maida martani ga masu kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya cire shi daga mukaminsa
  • Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ya jaddada cewa Shugaba Tinubu na da yanci da karfin ikon tsige shi daga matsayin minista idan ya ga dama
  • Ya kuma tabo tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, yana mai cewa ba zai samu kuri'u a Ribas ba idan ya fito takara a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da cikakken ’yanci da ikon korarsa daga mukaminsa a duk lokacin da ya ga dama.

Wike ya bayyana haka ne a matsayin raddi ga masu kiraye-kirayen shugaban kasa ya cire shi daga matsayin minista domin a samu masalaha a rikicin siyasar jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna, Sanata Dickson ya koma jam'iyyar hadaka, ADC? Gaskiya ta fito

Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike Hoto: @govwike
Source: Twitter

Wike ya maida martani ga masu sukarsa

Tribune Online ta tattaro cewa Wike ya maida martani ne a ranar Lahadi yayin bikin rufe rangadin godiya da yake yi a kananan hukumomin Jihar Rivers.

A cewarsa, goyon bayan da ya bai wa Shugaba Tinubu a zaben 2023 ya samo asali ne daga yarda da hangen nesan shugaban, inda ya ce ba su taba kulla wata yarjejeniya ta musamman da Tinubu ba kafin zaben.

“Ba mu yi wata yarjejeniya da shugaban kasa ba a 2023. Abin da kawai ya ce mana shi ne mu ba shi goyon baya, ba za mu yi nadama ba. Mun ba shi goyon bayan, kuma da ikon Allah, ya ga abin da muka yi,” in ji Wike.

Wike ya jaddada goyon baya ga Tinubu

Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya nuna godiya ga mutanen Rivers ta hanyar ba su mukamai da tallafi, yana mai ambaton nadin da aka yi masa a matsayin Ministan Abuja a matsayin misali.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Matakin da Tinubu ya dauka bayan alaka ta sake tsami tsakanin Wike da Fubara

Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da ba Tinubu cikakken goyon baya domin ya samu nasarar sauke nauyin da ke kansa, in ji Vanguard.

Ministan Abuja ya waiwayi Atiku

Wike ya soki magoya bayan tsohon dan takarar shugaban kasa na PDP a 2023, Atiku Abubakar, yana mai cewa Atiku bai samu fiye da kashi 10 cikin 100 na kuri’un Rivers ba a zaben da ya gabata.

Ya gargadi Atiku, wanda yanzu ya koma jam’iyyar ADC, cewa zai fuskanci irin wannan koma baya a Rivers idan ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.

Atiku da Wike.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Ministan Abuja, Nyesom Wike Hoto: @Atiku, @Govwike
Source: Facebook

Tinubu zai gana da Wike da Fubara

A wani rahoton, kun ji cewa alamu sun nuna cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakani a rikicin da ke gudana tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara, da Ministan Abuja, Nyesom Wike.

A cewar wata majiya mai matukar inganci, Shugaba Tinubu ya gayyaci Wike domin tattaunawa kan rikicin Ribas, amma ana ganin za a yi wannan zama ne a kasar waje.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas, waɗanda ake cewa suna biyayya ga Wike, suka kaddamar da sabon yunkurin tsige Gwamna Fubara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262