Babbar Magana: An Bukaci Gwamna Mutfwang Ya Yi Murabus daga Kujerarsa
- Tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang ya nuna damuwa kan yadda yan siyasa ke sauya jam'iyya bayan sun samu mulki a Najeriya
- Jang ya bukaci Gwamna Caleb Mutfwang ya bar wa PDP kujerarsa saboda a inuwarta ya ci zabe a shekarar 2023
- Ya kuma soki hukumar INEC bisa zargin katsalandan a harkokin jam'iyyun siyasa, yana mai cewa hakan barazana ce ga dimokuradiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau, Nigeria - Tsohon Gwamnan Filato kuma jagoran jam’iyyar PDP a jihar, Jonah David Jang, ya bukaci Gwamna Caleb Mutfwang ya yi murabus daga kujerarsa.
Jang ya ce kamata ya yi Gwamna Mutfwang ya yi murabus, sannan ya sake tsayawa takarar gwamna, saboda ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Source: Facebook
Rahoton Daily Trust ya ce Jonah Jang ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP, lokacin da yake martani kan matakin Gwamna Mutfwang na komawa APC.
An nemi Gwamna Mutfwang ya yi murabus
A cewarsa, tun da gwamnan ya yanke shawarar barin jam’iyyar da ta kawo shi mulki, ya kamata ya ajiye mukaminsa, ya koma sabuwar jam’iyyar, sannan ya nemi sabon izini daga jama’a ta hanyar zaɓe.
Jang ya ce:
“Ban san daga ina muka samo tunanin ɗaukar amanar da jama’a suka ba mu, mu kai ta wani wuri ba tare da tunani ba.
"Ya kamata mutum ya fara yin murabus, a shirya sabon zaɓe, sannan ya sake tsayawa takara a sabuwar jam’iyyar da ya koma. Wannan shi ne ainihin dimokuraɗiyya,” in ji Jang.
Jang ya tuna wahalar da suka yi a Filato
Ya kara kara da cewa Mutfwang na zaune a kujerar gwamnan Filato ta sanadiyyar jam'iyyar PDP, wacce ita ce tsanin da ya taka ya samu mulki.
“Mu ne muka kawo Caleb Mutfwang mulki. Kafin ya watsar da mu, dole ne ya kammala wa’adinsa tare da mu.
"Ba zai yiwu ya ɗauki hakkinmu ya kai wani wuri ba. Mu muka yi kamfen, mu muka zabe shi, muka kafa gwamnati karkashin inuwar PDPi,” in ji shi.
Me ke jawo yawan sauya sheka a Najeriya?
Jang ya kuma dora laifi kan tsarin siyasar Najeriya da ke bai wa ‘yan siyasa damar sauya sheka ba tare da rasa mukamansu ba, yana mai cewa hakan na lalata dimokuraɗiyya.
“Ban taba ganin sunan mutum a takardar zaɓe ba, jam’iyya ce ake rubutawa. Jam’iyya ce ke cin zaɓe, ba mutum ba.
"Najeriya ce kaɗai ƙasar da mutum ke cin zaɓe da jam’iyya, daga bisani ya sauya sheka zuwa wata jam’iyya,” in ji Jang.

Source: Facebook
Har ila yau, tsohon gwamnan ya nuna damuwa kan abin da ya kira yunkurin maida ƙasar zuwa tsarin jam’iyya ɗaya, yayin da gwamnonin jihohi ke ta tururuwa zuwa jam’iyyar mulki.
Ya kuma zargi INEC da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na jam’iyyar PDP, yana mai cewa hakan barazana ce ga dimokuraɗiyya, kamar yadda Vanguard ta kawo.
PDP ta soki sauya shekar Gwamna Mutfwang
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP reshen jihar Plateau ta nuna rashin jin dadinta bayan sauya shekar Gwamna Caleb Mutfwang zuwa APC.

Kara karanta wannan
"Ni zan masu dariya a karshe," Kwankwaso ya kara tabo batun sauya shekar Gwamna Abba
PDP ta ce ta ɗauki ficewar Gwamna Caleb Mutfwang daga jam’iyyar a matsayin cin amana da kuma yaudarar al’ummar da suka yarda da shi.
Babbar jam'iyyar adawa ta kara da cewa Gwamna Mutfwang ya zaɓi fifita burinsa na kashin kansa a kan muradun al’ummar Filato.
Asali: Legit.ng

