Jam'iyyar APC Ta Sanya Lokacin Gudanar da Babban Taronta na Kasa
- Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya za ta gudanar da babban taronta na kasa a cikin shekarar 2026 mai shirin kamawa
- APC za ta gudanar da babban taron ne domin zaben shugabannin wadanda za su ci gaba da jan ragamar harkokinta
- Kafin babban taro na kasa, za a fara da zabar shugabanni a matakin gunduma, kananan hukumomi da jihohi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam'iyyar APC ta fitar da cikakken jadawalin shirye-shiryen gudanar da babban taronta na kasa.
Jam'iyyar APC za ta gudanar da taron ne domin zaben shugabannin da za su ci gaba da jan ragamarta.

Source: Twitter
Sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata Ajibola Basiru, ne ya fitar da jadawalin a shafinsa na X a ranar Asabar, 19 ga watan Disamban 2025.
APC za ta zabi shugabanni

Kara karanta wannan
Duk da samun jihohi 28, Shugaba Tinubu ya hango matsalar da ta tunkaro jam'iyyar APC
A cewar jadawalin, aikin zai fara ne da fara rajistar mambobin ta na’ura daga ranar Litinin, 1 ga Disamba, 2025, zuwa 30 ga Janairu, 2026.
Bayan haka, za a fitar da sanarwar tarurrukan jam’iyya ga rassan jihohi da na babban birnin tarayya a ranar, 2 ga watan Fabrairun 2026.
Jadawalin ya nuna cewa saya da mika takardun neman tsayawa takara na tarurrukan gundumomi da kananan hukumomi za su gudana daga ranar 4 zuwa 9 ga watan Fabrairu, 2026.
Haka kuma, za a kaddamar da kwamitocin tantance ’yan takara na mukaman gundumomi da kananan hukumomi a ranar 10 ga Fabrairu, yayin da tantancewar ’yan takara za ta gudana daga 11 zuwa 13 ga Fabrairu.
An saka taron gundumomi a ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026, yayin da za a saurari ƙorafe-ƙorafen da suka taso daga tarurrukan gundumomi a ranar 19 ga Fabrairun 2026.
Tarurrukan kananan hukumomi, ciki har da zaɓen wakilai uku zuwa babban taron kasa, inda dole ɗaya ta kasance mace ce, za su gudana a ranar 20 ga Fabrairu, tare da sauraron korafe-korafe a ranar 21 ga Fabrairun 2026.
Yaushe za a gudanar da zabe a matakin jiha?
A matakin jiha, saya da mika takardun neman mukaman shugabannin jam’iyya na jiha za su fara tun daga 23 zuwa 27 ga Fabrairu, 2026.
Tantancewa da sauraron korafe-korafe na shugabannin jihohi za su gudana a karshen Fabrairu da farkon Maris, yayin da tarurrukan jihohi za su kasance a ranar Asabar, 7 ga Maris, 2026.
Jadawalin ya nuna cewa korafe-korafen tarurrukan jihohi za a saurare su daga 9 zuwa 11 ga Maris, 2025.

Source: Twitter
Za a gudanar da babban taron APC a 2026
Daga nan jam’iyyar za ta wuce matakin shiyya, inda saya da miƙa takardun neman tsayawa takara na tarurrukan shiyya da babban taron kasa za su gudana daga ranar 12 zuwa 17 ga watan Maris, 2026.
Za a kaddamar da tarurrukan shiyya a ranar 18 ga Maris, sai tantance ’yan takara a ranakun 19 da 20 ga Maris 2026.
An tsara cewa tarurrukan shiyya a dukkan shiyyoyi shida na kasar nan su gudana a ranar Asabar, 21 ga Maris, 2026.
A ƙarshe, jadawalin ya nuna cewa babban taron kasa na APC zai gudana daga ranar Laraba, 25 ga watan Maris, zuwa Asabar, 28 ga watan Maris, 2026.
Gwamna Mutfwang ya koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya fice daga jam'iyyar APC mai adawa a Najeriya.
Gwamna Mutfwang ya koma jam'iyyar APC mai mulki bayan ficewarsa daga PDP wadda ya lashe zaben gwamna karkashinta a shekarar 2023.
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yelwata, ya sanar da ficewar Gwamna Mutfwang daga jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng

