Zaben Anambra: Dan Takarar APC Ya Bayyana Matsayarsa kan Nasarar Gwamna Soludo
- Dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Anambra, Prince Nicholas Ukachukwu, ya yi magana bayan rashin nasarar da ya yi
- Prince Nicholas Ukachukwu ya koka kan yadda aka rika tsangwama da muzgunawa magoya bayansa
- Dan takarar na APC ya kuma bayyana matsayarsa kan yiwuwar kalubalantar sakamakon zaben wanda aka gudanar a ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamban 2025
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Anambra - Ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar Anambra da aka gudanar a ranar Asabar, Prince Nicholas Ukachukwu, ya koka kan muzgunawa magoya bayansa.
Prince Nicholas Ukachukwu ya nuna bakin cikinsa kan kona gidan wata mai goyon bayansa a karamar hukumar Anambra ta Gabas.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta ce dan takarar na APC ya bayyana hakan ne bayan kammala zaben gwamnan da aka gudanar.

Kara karanta wannan
Zaben Anambra: Dan takarar ADC ya gano lam'a a zabe, ya ce bai gamsu da sakamako ba
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ukachukwu ya koka kan tsangwamar 'yan APC
A cewarsa, laifin matar shi ne nuna goyon baya ga jam’iyyar APC duk da barazanar da ta fuskanta daga sauran jam’iyyu.
Ko da yake bai bayyana sunanta ba, Ukachukwu ya ce zaɓen ya tabbatar da cewa jam’iyyar APC tana da tushe a Anambra, duk da ikirarin jam’iyyun adawa cewa APC ba ta da karfi a jihar.
Ya bayyana cewa an lalata motoci da gine-ginen magoya bayan jam’iyyar a lokacin yakin neman zaɓe, yana mai cewa gwagwarmayar ba ta kare ba tukuna.
Ya batun zuwa kotu?
Dangane da yiwuwar kalubalantar sakamakon zaɓen, Ukachukwu ya ce har yanzu suna tattara bayanai daga mazabu zuwa kananan hukumomi kafin yanke hukunci tare da jam’iyyar APC.
“A halin yanzu muna tattara bayanai da shaidun da suka shafi zaɓen. Kuma babu wani mataki da zan ɗauka ba tare da shawarar jam’iyyata ta APC ba. Ita ce za ta yanke hukunci kan matakinmu na gaba.”
“Duk da abin da ya faru, ina godiya ga magoya bayana, mambobin APC da abokai saboda jajircewarsu a lokacin yakin neman zaɓe da lokacin zaɓen kansa.”
“Abin da ya fi daga min hankali shi ne kona gidan wata mai goyon bayana a Anambra ta Gabas saboda jajircewarta duk da barazana da tsangwama daga jam’iyyun adawa.”
“An kona gidan matashiyar ne saboda ta tsaya tsayin daka. A lokacin kamfen kuma an kona wasu motocin da gine-ginen magoya bayanmu, amma duk da haka sun ci gaba ba su karaya ba, kuma ina matukar godiya.”
- Prince Nicholas Ukachukwu

Source: Twitter
Ya kara da cewa bayan tattara bayanai da shawarar jam’iyyar APC, za su yanke hukuncin mataki na gaba game da yadda za su bi lamuran zaɓen.
Dan takarar ya yi watsi da sakamakon zabe
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar jam'iyyar LP a zaben gwamnan jihar Anambra, Dr. George Moghalu, ya yi fatali da sakamakon zaben.
Dr. George Moghalu ya yi zargin cewa ba a gudanar da sahihin zabe ba a zaben na ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamban 2025.
Hakazalka ya yi zargin cewa an yi amfani da kudi don sayen kuri'u tare da barin kananan yara su kada kuri'a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

