Zaben Anambra: Dan Takarar ADC Ya Gano Lam'a a Zabe, ya Ce Bai Gamsu da Sakamako Ba
- Dan takarar gwamna a ADC a jihar Anambra y ace sam bai gamsu da zaben da aka gudanar ranar Asabar ba
- Nwosu ya bayyana yadda aka yi cinikin kuri’u da kuma musayar kudi don tabbatar da zaben jam’iyyar APGA
- A gefe guda, shugaba Tinubu ya bayyana murna da jin dadi yayin da Soludo ya sake nasara a zaben na Anambra
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Jihar Anabmra - John Nwosu, dan takarar jam’iyyar ADC a zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 8 ga Nuwamba a jihar Anambra, ya yi watsi da sakamakon zaben yana mai cewa “ba gaskiya ba ne kuma an tauye muradin jama’a gaba daya.”
A cewar sakon da ya fitar bayan kammala zaben, Nwosu ya ce an jirkita tsarin zaben ta hanyar sayen kuri’u da cin hanci a kusan dukkanin rumfunan zabe a fadin jihar.
Idan baku manta ba, an sanar da cewa, dan takarar jam’iyyar APGA), Charles Soludo ne ya lashe zaben da kuri’u 422,664, yayin da Nicholas Ukachukwu na APC ya samu kuri’u 99,445, sai kuma Nwosu wanda ya samu kuri’u 8,208 kacal.

Source: Twitter
Farfesa Edoba Omoregie, wanda shi ne Shugaban Jami’ar Benin kuma Jami’in tattara sakamakon zabe na INEC, shi ne ya bayyana sakamakon a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ban gamsu da sakamakon ba, Nwosu
Amma Nwosu ya dage cewa mutanen Anambra ba su samu ra’ayinsu ba, yana zargin cewa zaben ya zama kasuwanci maimakon dimokuradiyya, inda ake bai wa masu kada kuri’a kudi daga N3,000 zuwa N20,000.
A kalamansa:
“Wannan abin kunya ne ga kasa da kuma cin zarafin dimokuradiyyarmu. Nasara da aka saya da kudi, ba nasara ba ce, illa asara ga gaskiya da adalci.
“Gaskiyar nasara ba ta cikin sakamako, tana cikin tsarkin tsarin da aka bi. Zaben da ya cika da rashawa, magudi da cinikin kuri’a ba zai taba zama muradin jama’a ba.”
Akwai laifin hukumomi, inji Nwosu
Ya kuma soki hukumomi da sauran cibiyoyi da ya ce sun kasa kare amincin kuri’ar jama’a, yana mai cewa idanuwan duniya sun ga yadda adalci ya fadi kasa a zaben.
Ya gode wa jam’iyyarsa ADC, da kungiyar yakin neman zabensa, saboda tsayawa da gaskiya da kwarin gwiwa duk da tsoratarwa da tayin kudi.
Sai dai, ba karon farko kenan ba da ‘yan siyasa ke kalubalantar juna bayan zabe ba, hakan yakan faru a kusan karshen kowanne zabe.
Tinubu ya taya Soludo murna
A gefe guda, Shugaban kasa Bola Tinubu ya taya Gwamna Charles Soludo murnar sake lashe zaben gwamnan Anambra karo na biyu, yana mai cewa hakan shaida ce ta jagoranci nagari da amincewar jama’a gare shi.
A cikin wata sanarwa daga fadar shugaban kasa a Abuja, Tinubu ya ce nasarar Soludo ta kafa tarihi a siyasar Anambra, inda ya zama gwamna na uku da ya sake lashe wa’adi na biyu.
Ya kuma yaba da mutanen Anambra, jami’an tsaro da hukumar INEC saboda zabe cikin aminci kuma ya gudana cikin kwanciyar hankali.
A cewar Tinubu:
“Sake zaben Soludo shaida ce ta hangen nesa da jagoranci nagari. Ya nuna cewa ilimi da gaskiya suna iya canza mulki idan aka yi amfani da su cikin kwarewa da gaskiya.”
Irin ayyukan ci gaba da aka yi a Anambra
Ya kara da cewa, lokacin da ya kai ziyara jihar Anambra a watan Mayu, ya ga ayyukan ci gaba da Soludo ke aiwatarwa ci gaba.
Shugaban kasar ya bukaci Soludo da ya yi hakuri da masu adawa, ya kuma nemi hadin kai don ci gaban jihar.
Tinubu ya kuma yaba da sabon Shugaban INEC, Joash Amupitan, saboda gudanar da zabe mai inganci da gaskiya, yana mai cewa ya kamata hukumar ta ci gaba da kara kyautata tsarin ta domin karfafa dimokuradiyyar Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


