Anambra 2025: Soludo Ya Lallasa APC, LP, Ya Ci Zabe a Dukkan Kananan Hukumomi 21
- Gwamna Charles Soludo na jam'iyyar APGA ya samu nasarar lallasa APC, LP, PDP a zaben gwamnan jihar Anambra
- Sakamakon zaben da hukumar INEC ta bayyana a Awka ya nuna cewa Soludo ya lashe dukkan kananan hukumomi 21
- Yayin da aka bayyana sakamakon zaben, APGA ta tashi da kuri'u 422,664, sai APC da ke binta a baya da kuri'u 99,445
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta dawo ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Anambra.
A ranar Asabar, 8 ga watan Satumba, Legit Hausa ta rahoto cewa INEC ta gudanar da zaben gwamnan Anambra a kananan hukumomi 21.

Source: Original
Soludo ya lashe zabe a Anambra
Jami'in tattara sakamakon zabe na jihar Anambra, kuma shugaban jami'ar Benin, Farfesa Edogah Omoregie ne ya sanar da dage tattara sakamakon a baya, in ji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan dawo wa daga dan takaitaccen hutu, jami'in tattara sakamakon zabe daga karamar hukumar Anambra ta Yamma ya soma yin bayani.
A bayanin da ya yi, ya sanar da cewa dan takarar jam'iyyar APGA, kuma gwamnan Anambra, Charles Soludo ne ya lashe zabe a Anambra ta Yamma.
Anambra: Kuri'un da APGA, APC, suka samu
Yanzu da Charles Soludo ya lashe zabe a wannan karamar hukumar, hakan ya sa ya lashe dukkan zaben a kananan hukumomi 21 na jihar.
Yayin da aka bayyana sakamakon zaben dukkan kananan hukumomi 21, jam'iyyar APGA ta tashi da kuri'u 422,664, sai kuma APC da ke binta a baya da kuri'u 99,445.
Hakazalika, jam'iyyar LP ta samu kuri'u 10,505 a zaben yayin da PDP ta samu kuri'u 1,401, mafi kankanta a kuri'un da manyan jam'iyyun adawa a jihar suka samu.
Anambra: Hasashen 'yan Najeriya ya tabbata
Dama dai, Legit Hausa ta rahoto cewa 'yan Najeriya yi hasashen nasarar Gwamna Charles Soludo a wani zaben jin ra'ayi da aka yi a shafin X.
Kashi 53.5 na wadanda suka kada zaben ra'ayi da Legit.ng ta gudanar a soshiyal midiya su na ganin cewa Soludo ne zai ci zaben da aka yi a ranar Asabar.
Sannan 33.8% sun ce Moghalu Nnadubem na LP ne zai yi nasara, yayin da 7% suka nuna Nicholas Ukachukwu na APC zai ci zaben. Ezenwafor Jude na PDP ya samu kuri'a 5.6% kawai.

Source: Twitter
Soludo ya lashe kananan hukumomi 21
Gwamna Charles Soludo na jam’iyyar APGA ya lashe dukkanin kananan hukumomi 21 a zaben gwamnan jihar Anambra, kamar yadda muka ruwaito.
Hukumar INEC ta sanar da cewa APGA ta samu kuri’u 422,664, yayin da APC ta samu 99,445, LP 10,505, sannan PDP 1,401.
INEC ta ce za ta bayyana sakamakon karshe bayan kammala ƙididdigar da jami’an zabe ke yi a Awka, babban birnin jihar.
Jami'ar INEC ta suma a zaben Anambra
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata jami’ar INEC ta yanke jiki ta sume a yayin zaben gwamnan Anambra saboda hayaniya da matsalar na’urar BVAS.
An samu rahoto cewa dubban masu jefa kuri’a a Enugwu-Ukwu sun kasa kada kuri’unsu saboda BVAS ta gaza tantance katin masu zabe.
An ce jami’ar, Miss Blessing Egoigwe, ta sume ne yayin da jama’a suka fara hayaniya saboda gazawar na’urar BVAS wajen tantance katin masu zabe da kuma yatsun hannunsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

