Zaben Anambra 2025: Ƴan Takarar APC, LP, ADC, Sun Sha Kasa a Kananan Hukumominsu

Zaben Anambra 2025: Ƴan Takarar APC, LP, ADC, Sun Sha Kasa a Kananan Hukumominsu

  • Gwamna Charles Soludo ya doke George Moghalu na LP da John Chuma-Nwosu na ADC a mazabarsu ta Nnewi ta Arewa
  • Soludo ya samu kuri’u 20,320 yayin da Moghalu ya samu 1,140, shi kuma Chuma-Nwosu ya samu 553, in ji jami'in INEC
  • Nicholas Ukachukwu na APC shima ya sha kaye a mazabarsa ta Nnewi ta Kudu inda Soludo ya samu 17,286 kuri’u.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - Gwamna Charles Chukwuma Soludo ya yi nasara a mazabun gida na manyan abokan hamayyarsa biyu — George Moghalu na LP da John Chuma-Nwosu na ADC.

Soludo da jam'iyyarsa ta APGA sun samu wannan nasarar ne a zaben gwamnan jihar Anambra da aka gudanar ranar Asabar, 8 ga Nuwamba, 2025.

'Yan takarar APC, LP da ADC sun sha kashi hannun Soludo a kananan hukumominsu
Hoton gwamnan Anambra, Charles Soludo, Nicholas Ukachukwu da George Moghalu. Hoto: @CCSoludo, @Dr_N_Ukachu_MFR, @MoghaluGeorge
Source: Twitter

Nasarar Soludo a zaben jihar Anambra

Moghalu da Chuma-Nwosu sun kasance ‘yan asalin karamar hukumar Nnewi ta Arewa, yayin da Soludo ya fito daga Isuofia a karamar hukumar Aguata, in ji Premium Times.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra 2025: Jami'ar INEC ta yanke jiki ta suma ana tsakiyar kada kuri'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da suka yi tsammanin samun goyon bayan al'ummarsu a gida, sakamakon da INEC ta bayyana ya nuna Soludo ya fi karfi sosai a yankin.

Ko kafin sanar da sakamakon zaben na kananan hukumomin Nnewi ta Arewa da Nnewi ta Kudu, Gwamna Charles Soludo ya doke dan takarar LP, a rumfar zabensa da kuri’u 57.

Legit Hausa ta ruwaito cewa Gwamna Charles Soludo na jam'iyyar APGA ne ya lashe zabe a rumfar zaben ta Uruagu Ward 1, da ke karamar hukumar Nnewi ta Arewa.

Sakamakon zabe daga Nnewi ta Arewa

Da yake bayyana sakamakon a cibiyar tattara sakamakon jihar, jami’in INEC da ke tattara sakamakon Nnewi ta Arewa ya tabbatar da cewa Soludo ya lashe yankin da kuri’u 20,320.

Ga yadda sakamakon ya kasance:

  • APGA (Soludo) – 20,320 kuri’u
  • LP (Moghalu) – 1,140 kuri’u
  • APC (Ukachukwu) – 5,441 kuri’u
  • ADC (Chuma-Nwosu) – 553 kuri’u
  • YPP (Paul Chukwuma) – 1,100 kuri’u

Kara karanta wannan

Reshe zai juye da mujiya, Gwamna mai ci ya zargi 'yan adawa da sake kudi a zabe

Daga cikin kuri’u 29,284, an tabbatar da 28,715 a matsayin sahihai, yayin da 569 suka lalace.

Ukachukwu na APC ya sha kaye a Nnewi South

Hakazalika, Nicholas Ukachukwu na APC shima bai yi nasara a mazabarsa ba, domin Soludo ya samu 17,286 kuri’u, yayin da shi ya samu 9,281.

A cewar jami’in tattara sakamakon, 27,937 ne suka kada kuri’a daga cikin 102,907 da aka yi wa rajista.

APGA ta tabbatar da karfinta a Anambra

Wannan nasarar ta tabbatar da cewa APGA har yanzu ita ce babbar jam’iyyar da ke da karfi a jihar Anambra.

Masana siyasa sun ce, irin wannan nasarar a yankin manyan abokan hamayya na iya tabbatar da burin Soludo na samun tazarce a matsayin gwamna.

Soludo ya samu nasara a kananan hukumomin da 'yan takarar APC, LP da ADC suka fito a Anambra.
Gwamna Charles Soludo ya na jawabi ga al'ummar jihar Anambra. Hoto: @CCSoludo
Source: Twitter

An dage tattara sakamakon zaben Anambra

Tun da fari, mun ruwaito cewa, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta dage tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Anambra da aka kada.

Shugaban tattara sakamakon zaben Anambra, kuma shugaban jami'ar Benin, Farfesa Edogah Omoregie, ya sanar da dage tattara sakamakon.

Kara karanta wannan

Anambra 2025: APGA ta lallasa APC, PDP, ta lashe zabe a rumfar dan takarar LP

Farfesa Edogah Omoregie ya sanar da dage tattara sakamakon ne a safiyar Lahadi, a hedikwatar hukumar da ke Awka, babban birnin Anambra.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com