INEC Ta Ɗage Tattara Sakamakon Zaben Gwamnan Anambra, Ta Sanya Sabon lokaci
- INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaben gwamnan Anambra yayin da ake jiran sauran kananan hukumomi biyu
- Farfesa Edogah Omoregie, jami’in tattara sakamakon jihar, ya ce an kammala tattara sakamakon kananan hukumomi 19
- Gwamna Charles Soludo na APGA na kan gaba da kuri’u 389,789, inda yake kan hanyar lashe zabe a karo na biyu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dakatar da tattara sakamakon zaben gwamnan Anambra da aka gudanar a ranar Asabar.
An dakatar da tattara sakamakon ne bayan kammala bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi 19 daga cikin 21 da ke jihar.

Source: Twitter
INEC ta dakatar da tattara sakamakon zabe
Jami’in tattara sakamakon jiha, Farfesa Edogah Omoregie na jami’ar Benin, ne ya sanar da hakan da safiyar Lahadi a cibiyar hukumar da ke Awka, babban birnin jihar, in ji rahoton Punch.
Ya bayyana cewa tattara sakamakon zai ci gaba da karfe 6:00 na safe, yayin da ake jiran sakamakon kananan hukumomi biyu.
An rahoto cewa jami'an tattara sakamakon zaben kananan hukumomin biyu ba su kai ga isowa cibiyar ba saboda jinkiri wajen isar da kayan aikin zabe da kuma nisan wuraren.
“Mun kammala tattara sakamakon kananan hukumomi 19, saura biyu da muke jiran sakamakonsu. Don haka za mu dakata, sai zuwa karfe 6:00 na safiya za mu ci gaba."
- In ji Farfesa Omoregie.
Anambra: Soludo ya samu kuri'u masu yawa
Har zuwa lokacin da aka dakatar da tattara sakamakon, dan takarar jam’iyyar APGA, Gwamna Charles Chukwuma Soludo, shi ke kan gaba da babban rinjaye a zaben.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa, sakamakon kananan hukumomi 19 da aka bayyana ya nuna cewa:
- APGA (Soludo) na da kuri'u 389,789.
- APC (Nicholas Ukachukwu) na da kuri'u 91,592.
- LP (George Moghalu) na da kuri'u 10,366.
- PDP (Jude Ezenwafor) na da kuri'u 1,230.
Wannan sakamakon ya nuna cewa Soludo yana da rinjaye sosai, kuma yana da dama mai karfi ta samun nasara idan sakamakon saura kananan hukumomin biyu bai zo da babban sauyi ba.

Source: Facebook
INEC ta dora 95% na sakamakon zaben Anambra
INEC ta bayyana cewa ana gudanar da tattara dukkanin sakamakon zaben ne a cibiyarta da ke Awka, inda sakamakon daga rumfunan zabe ke isa daga sassan jihar.
Hukumar ta kara tabbatar da cewa an riga an loda kashi 95 cikin 100 na sakamakon zaben a shafinta na IReV, wanda ke tabbatar da gaskiya da ingancin tsarin.
INEC ta ce na'urar BVAS da aka yi amfani da ita ta taimaka wajen rage kura-kurai da karfafa sahihancin zabe, tare da ba da tabbacin cewa sakamakon karshe zai kasance mai gaskiya.
Asali: Legit.ng

