"Annabi SAW Ya Ba Ni Izini," 'Dan Sheikh Dahiru Bauchi Ya Fito Takarar Gwamna a 2027

"Annabi SAW Ya Ba Ni Izini," 'Dan Sheikh Dahiru Bauchi Ya Fito Takarar Gwamna a 2027

  • Matashi kuma dan malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya fito takarar gwamnan Bauchi a zaben 2027 mai zuwa
  • Naziru Dahiru Bauchi ya nuna cewa ya dauki wannan mataki ne bayan ya samu izini daga Manzon Allah, Annabi Muhammad SAW
  • 'Dan fitaccen malamin ya ce ya nemi zabin Allah, yana mai cewa yana fatan zama magajin Sanata Bala Muhammed domin dorawa daga inda ya tsaya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Daya daga cikin 'ya'yan fitaccen malamin Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shirya tsayawa takarar gwamnan Bauchi.

'Dan babban malamin addinin musuluncin mai suna, Naziru Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ayyana shirinsa na neman takarar gwamnan jihar a zaben 2027 mai zuwa.

Sheikh Dahiru Bauchi.
Hoton Sheikh Dahiru Usman Bauchi tare da dansa Naziru Hoto: Naziru Tahir
Source: Facebook

Naziru Dahiru Bauchi ya tabbatar da hakan ne a wani bidiyo da wallafa a shafinsa na Facebook, inda aka gan shi a kusa da masallacin Harami da ke Makkah a Saudiyya.

Kara karanta wannan

Dalilin Peter Obi na zagaya Najeriya, ya na ba makarantu kyautar miliyoyin Naira

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan Sheikh Dahiru Bauchi zai fito takara

Ya bayyana cewa ya yanke shawarar neman takarar gwamnan Bauchi ne bayan ya samu izini daga Manzon Allah (SAW).

'Dan malamin ya ce bayan ya nemi izinin Annabi SAW kuma ya yi sallar neman zabin Allah watau Istikhara, ya fahimci cewa wannan ne lokacin da ya dace ya nemi mulkin Bauchi.

Naziru ya kara da cewa yanzu lokaci ne da ya kamata matasa su fito su karbi ragamar mulki domin kawo sauyi da ci gaba a rayuwar al'umma.

Ya karkare da cewa yana fatan yi wa al'ummar jihar Bauchi adalci tare da dorawa daga ayyukan da Sanata Bala Mohammed, Kauran Daular Usmaniyya ya yi.

Ya kuma yi addu'ar Allah ya kare Bauchi daga dukan masu nufarta da sharri, inda ya nanata cewa Annabi ya yi masa izinin neman takarar gwamnan Bauchi a zaben 2027.

Cikakken jawabin 'dan Sheikh Dahiru Bauchi

A bidiyon, wanda ke yawo a kafafen sada zumunta, Naziru Dahiru Bauchi ya ce:

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau ya yi magana kan lokacin da zai daina siyasa

"Assalamu Alaikum, ina mai bayyana aniyata ta tsayawa takarar gwamnan Bauchi a shekarar 2027 bayan na nemi izinin Manzon Allah SAW a Madina kuma na ziyarci dakin Allah a Makkah.
"Na yi Istikhara na ga cewa yanzu zamanin mu ne matasa, muna fatan Allah Ya sa mu yi wa al'ummar jihar Bauchi adalci, Allah ya ba mu ikon dorawa daga ayyukan da Sanata Bala Muhammed, Kauran Daular Usmaniyya ya yi, mu kara inganta su.
"Allah Ya kiyaye Bauchi daga shiga hannun wadanda za su wargaza ta, Allah ya kare Najeriya, yanzu zamanin mu ne tun da Manzon Allah ya yi izini, mun nemi zabin Allah kuma an nuna mana nasara, Allah Ya ba mu nasara."
Naziru Sheikh Dahiru Bauchi.
Hoton 'dan Sheikh Dahiru Bauchi, Naziru yana karatu Hoto: Naziru Tahir
Source: Facebook

Dahiru Bauchi ya godewa shugaban Aljeriya

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya mika sakon godiya ga Shugaban Ƙasar Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune.

Fitaccen malamin addinin Musuluncin ya yi wannan godiya ne bisa amincewa da bayar da guraben karatu kyauta ga ɗalibai 140 daga Najeriya a jami’o’in da ke Aljeriya.

Malamin ya kuma yaba da irin jagorancin Shugaban Aljeriya, yana mai cewa irin wannan shugabanci abin koyi ne ainun ga sauran ƙasashen duniya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262