Matasan Arewa Sun Fadi Matsayarsu bayan an Fara Kiran Shugaban APC Ya Yi Murabus

Matasan Arewa Sun Fadi Matsayarsu bayan an Fara Kiran Shugaban APC Ya Yi Murabus

  • Wata kungiya ta yi kira ga shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi murabus daga mukaminsa
  • Sai dai, wata kungiyar matasan Arewa ta yi watsi da wannan kiran wanda ke neman shugaban na APC ya yi murabus
  • Kungiyar ta bayyana cewa masu yin kiraye-kirayen ba su da hurumin yin hakan saboda ba 'yan jam'iyyar APC bane

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kungiyar matasan Arewacin Najeriya mai suna Northern Nigeria Youth Leaders Forum (NNYLF) ta yi martani kan bukatar shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi murabus.

Kungiyar ta yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi na neman Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar APC.

Kungiya ta bukaci Nentawe Yilwatda ya yi murabus daga shugabancin APC
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

Tashar Channels tv ta ce shugaban kungiyar na kasa, Murtala Gamji, ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai a Abuja.

Kara karanta wannan

ADC ta samu karuwa a Kano, tsohon dan majalisa ya fice daga APC zuwa jam'iyyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Murtala Gamji ya ce mutanen da ke neman Yilwatda ya sauka ba su wakiltar ainihin muradun mambobin jam’iyyar APC.

Kungiyar ta jaddada cewa waɗanda ke bayan wannan kira ba su da cancanta ko matsayin siyasa da zai ba su damar yin irin wannan bukatar ba.

An bukaci Nentawe ya yi murabus

A baya-bayan nan ne wata ƙungiya mai suna All Progressives Congress Youth Solidarity Network (APC-YSN), ƙarƙashin jagorancin Comrade Danesi Momoh Prince, ta bai wa Farfesa Yilwatda makonni biyu ya yi murabus ko kuma su yi zanga-zanga.

Ƙungiyar ta zargi Yilwatda da gazawa a fagen shugabanci, tana cewa shaharar jam’iyyar APC na ƙara raguwa a kullum a lokacin mulkinsa, abin da ke iya barazana ga nasarar sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Kungiya ta kare shugaban APC na kasa

Amma a martanin da kungiyar NNYLF karkashin jagorancin Murtala Gamji ta bayyana kungiyar da ke kira da a sauke Yilwatda a matsayin ‘yan jam’iyyar PDP da ke neman haifar da rudani a cikin APC.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: PDP ta dare gida 2, an dakatar da shugaban jam'iyya na kasa da kan shi

“Mutumin da ke kira ga shugabanmu na kasa ya yi murabus ma ba ɗan APC ba ne. Mun yi makaranta tare a ABU Zaria. Mutum ne daga Auchi kuma ɗan jam’iyyar PDP."
"Har ma PDP ta hukunta shi a Auchi, jihar Edo. Don haka, ba mu san alakarsa da shugabanmu mai mutunci ba."

- Murtala Gamji

Ya jaddada cewa kwanan nan aka nada Farfesa Nentawe Yilwatda, kuma tun daga lokacin ya jawo manyan ’yan siyasa zuwa jam’iyyar APC, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar da labarin.

Ya yi gargadin cewa ba za su lamunci wani yunkuri na tayar da fitina a shugabancin jam’iyyar ba.

An kare Nentawe kan zargin hana gwamnan Plateau shiga APC
Farfesa Nentawe Yilwatda wanda ke shugabantar jam'iyyar APC Hoto: Prof Nentawe Yilwatda
Source: Twitter

An wanke Nentawe daga zargi

Murtala Gamji ya kuma karyata zargin cewa Yilwatda yana hana Gwamna Caleb Mutfwang shiga jam’iyyar APC, kamar yadda APC-YSN ta yi ikirari, yana cewa hakan ba gaskiya ba ne.

“Shugaban jam’iyya mutum ne mai ra’ayin dimokuraɗiyya, kuma ba zai hana kowane gwamna shiga jam’iyya ba. Gwamnan kansa ya bayyana cewa ana matsa masa lamba ya shiga APC, to babu wanda ke hana shi."

- Murtala Gamji

Tsohon dan majalisa ya fice daga APC

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya fuskanci matsala a shirin takarar shugabancin jam'iyyar PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan majalisar wakilai daga jihar Kano, Hon. Nasiru Baballe Ila, ya fice daga jam'iyyar APC.

Hon. Nasiru Baballe Ila ya koka kan yadda aka rika nuna masa wariya tare da magoya bayansa a jam'iyyar APC.

Tsohon dan majalisar ya bayyana cewa ya koma jam'iyyar ADC mai adawa domin ci gaba da siyasarsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng