'Goodluck Jonathan Zai Yi Takara kuma Ya Lashe Zabe a Shekarar 2027'
- Ana ci gaba da maganganu kan yiwuwar tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya sake fitowa takara a zaben 2027
- Tsohon ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Farfesa Jerry Gana, ya bada tabbaci kan yiwuwar yin takarar Jonathan
- Ya nuna cewa 'yan Najeriya sun ga canji daga wajen shugabanni biyun da suka mulki kasar nan bayan tsohon shugaban kasan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Neja - Tsohon ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Farfesaa Jerry Gana, ya yi magana kan takarar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, a 2027.
Farfesa Jerry Gana ya tabbatar da cewa Jonathan zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2027 a karkashin jam’iyyar PDP, tare da komawa kan kujerar shugabanci.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa tsohon ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan taron zaben shugabannin PDP na jihar Neja a Minna a ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Jerry Gana ya ce kan takarar Jonathan?
Farfesa Jerry Gana ya ce ‘yan Najeriya sun gwada shugabanni biyu bayan Jonathan, kuma yanzu suna kaunar dawowarsa kan karagar mulki.
“A shekarar 2015, tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya ce burinsa bai kai a zubar da jinin ɗan Najeriya ba. Bayan ga wuce wani Shugaba ya yi mulki na tsawon shekaru takwas, yanzu kuma wani ya shafe shekaru biyu."
"‘Yan Najeriya sun ga bambanci, kuma bambancin ya fito fili. Yanzu suna maganar mu mu dawo musu da abokinmu, tsohon Shugaba Goodluck Jonathan."
"Zan iya tabbatar muku cewa Goodluck Ebele Jonathan zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027 a matsayin ɗan takarar PDP, kuma ya kamata mu shirya mu kaɗa masa kuri’a domin ya dawo kujerar shugabanci."
- Farfesa Jerry Gana
PDP ta samu yabo
Tsohon ministan ya bayyana PDP a matsayin jam’iyya mai sahihancin dimokuraɗiyya kuma mai dogaro da talakawa.
Farfesa Jerry Gana ya ce jam’iyyar ta kasance mai ba ‘yan Najeriya damar zaɓar shugabanninsu cikin ‘yanci.

Source: Getty Images
Ya kuma tabbatar da cewa PDP na ci gaba da samun karɓuwa a wajen 'yan Najeriya, saboda shirye-shiryenta da ke mayar da hankali ga al’umma.
Game da harkokin cikin gida na jam’iyyar, tsohon ministan ya musanta jita-jitar cewa akwai rikici, yana mai cewa an daɗe da warware dukkan sabanin da ake da shi.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su farka daga barci su kawar da gwamnatin yanzu, sannan su maye gurbin ta da dawowar Jonathan domin samun kyakkyawan mulki.
Jonathan ya gana da shugaban ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya ziyarci shugaban jam'iyyar ADC na kasa, Sanata David Mark.
Goodluck Jonathan ya ziyarci tsohon shugaban majalisar dattawan ne a gidansa da ke birnij tarayya Abuja, a daren ranar Alhamis, 25 ga watan Satumban 2025.
Ziyarar da tsohon shugaban kasan ya kai na zuwa ne jim kadan bayan jam'iyyar ADC ta kammala wani muhimmin taro da shugabanninta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

