Gwamnan PDP Ya Yi Magana kan Komawa ADC bayan Rashin Samun Mafaka a APC
- Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi magana kan batun sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar ADC
- A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakinsa ya fitar, ya bayyana cewa akwai mutanen da ke tsoron karbuwar da ya samu a wurin jama'a
- Gwamna Adeleke ya tabbatar da cewa zai tsaya takara a zaben gwamna na shekarar 2026 a karkashin inuwar PDP
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi magana kan jita-jitar cewa zai sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa ADC.
Gwamna Adeleke ya sake nesanta kansa daga batun komawa ADC, inda ya tabbatar da cewa har yanzu yana nan daram a jam’iyyar PDP.

Source: Twitter
Adeleke ya musanta batun komawa ADC
Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Olawale Rasheed, ya fitar a ranar Laraba, 17 ga watan Satumban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Olawale Rasheed ya bayyana cewa rahoton sauya shekar karya ce da wasu ke yadawa domin tayar da rudani a zukatan jama’a.
Mai magana da yawun gwamnan ya bayyana cewa masu yada rahoton, suna yi ne saboda tsoron farin jinin da yake kara samu a jihar Osun, rahoton The Punch ya tabbatar da labarin.
Gwamna Adeleke zai tsaya takara a 2026
Gwamna Adeleke ya jaddada cewa zai tsaya takara a zaben gwamna na 2026 a karkashin PDP, kuma jam’iyyar ta riga ta fara aiki domin tabbatar da nasarar sake zabensa.
"Hankalinmu ya kai kan wani rahoto mai cewa Gwamna Ademola Adeleke yana shirin komawa jam'iyyar ADC."
"Rahoton ba kawai karya ba ne, amma wani yunkuri ne da masu tsoron farin jinin gwamnan ke yi don kawo rudani a zukatan mutanen jihar Osun."
"Muna so mu sake tabbatar da cewa Gwamna Adeleke yana cikin PDP kuma baya da shirin komawa ADC ko wata jam'iyya."
"A halin yanzu, damuwarsa ita ce ci gaba da kawo wa al’ummar Osun, wadanda su ka ba shi kuri'unsu shekara uku da suka gabata romon dimokuradiyya."
"Muna kira ga jama’a da su yi watsi da rahoton da ke danganta Gwamna Adeleke da sauya sheka domin karya ce tsantsa. Gwamna Adeleke ba zai yi abin da ya saba wa muradin al’ummar Osun ba."
- Olawale Rasheed

Source: Twitter
Gwamna Adeleke ya ce da shi da shugabannin PDP a jihar suna mayar da hankali ne wajen karfafa jam’iyyar, musamman ta fuskar rajistar masu kada kuri’a da ake gudanarwa yanzu, domin tabbatar da nasara a zaben 2026.
Gwamna Adeleke ya fusata kan daurin Sarki
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya nuna rashin jin dadinsa kan daure wani basaraken jihar a kasar Amurka.
Gwamna Adeleke ya bayyana hukuncin zama gidan gyaran hali a kasar Amurka da aka yankewa Sarkin Ipetumodu, Mai martaba Joseph Oloyede, a matsayin abu mara dadi.
Hakazalika, gwamnan ya umarci kwamishinan harkokin kananan hukumomi da masarautun jihar, kan ya gaggauta daukar mataki kan lamarin.

Kara karanta wannan
'Yan hadaka na shirin sauya jam'iyya daga ADC zuwa ADA,? An ji yadda lamarin yake
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

