Tinubu: Dattawan Arewa Sun Fusata bayan Ikirarin APC kan Takarar 2027
- Ƙungiyar ACF ta ce kowanne ɗan Najeriya na da dama ya tsaya takarar shugabancin ƙasa, ba tare da la’akari da yanki ko jam’iyya ba
- ACF ta fadi haka ne a bayan ikirarin APC da ke nuna cewa Bola Ahmed Tinubu kawai ta yarda ya tsaya mata takara a 2027
- Kungiyar ta caccaki kalaman da ke cewa babu wanda zai tsaya takara da Tinubu a APC, tana cewa hakan ya sabawa tsarin mulki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Ƙungiyar ACF ta bayyana rashin amincewarta da kalaman wasu shugabannin jam’iyyar APC da ke cewa babu wanda zai tsaya takara da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Kungiyar ta yi mamakin kalaman, inda ta bayyana cewa kowane dan Najeriya da ke da sha'awar fito wa takara, ya cancanci a ba shi dama.

Source: Twitter
A wata hira da BBC Hausa, mai magana da yawun ACF, Farfesa Tukur Muhammad Baba, ya ce irin wannan magana ya sabawa tsarin mulkin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ACF ta caccaki kalaman APC
Kungiyar ACF ta bayyana cewa bai kamata irin wadannan kalamai su fito daga bakin shugabannin siyasa ba, musamman ma a cikin jam’iyya mai mulki.
A cewarsa, dimokuraɗiyya na buƙatar sahihanci da damar da kowane ɗan kasa zai samu, ba tare da ƙuntatawa bisa yanki, jam’iyya ko ƙabila ba.
Ya ce:
"Idan har ana bi tsarin doka da kundin tsarin mulki, duk wani dan Najeriya mai cikakken ‘yanci da ya cika sharuddan hukumar zabe, yana da ikon tsaya takara a duk matsayin da yake so," in ji Farfesa Baba.
Ya kara da cewa kungiyar ACF ba jam’iyyar siyasa ba ce, amma tana da burin ganin an gina demokuraɗiyya mai cike da adalci da damar kowa.
Martanin APC ga ACF
A martaninta, daraktan yaɗa labarai na jam’iyyar a ƙasa, Malam Bala Ibrahim, ya bayyana cewa tsarin mulki ya baiwa kowa dama, amma hakan ba yana nufin jam’iyya ba za ta fitar da wanda take so ba.
Ya ce:
“Kundin tsarin mulki bai hana kowa takara ba, amma jam’iyya na da ‘yancin fitar da wanda ta ke ganin ya fi dacewa ya wakilce ta."
Ya ce duk wanda ke sha’awar takara a karkashin APC, idan ya cika sharuddan jam’iyyar, zai samu dama ya fafata a zaben fidda gwani.

Source: Facebook
A watan Mayu, wasu jiga-jigan APC daga Arewa maso Yamma sun nuna goyon bayansu ga Shugaba Tinubu domin ya nemi wa’adi na biyu.
Sai dai kawo yanzu, Shugaban bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takara ba a hukumance, duk da ya kan nuna farin ciki idan ana fadin hakan a wurin taruka.
Musu ya kaure a tsakanin APC da PDP
A baya, kun ji cewa APC mai mulkin Najeriya da babbar jam’iyyar hamayya ta PDP sun shiga sabon rikici na siyasa, inda suka fara cacar baki kan zargin fara gangamin neman zabe.

Kara karanta wannan
Hukumar kwastam: Mutane kusan 600,000 sun nemi guraben aiki da ba su kai 4,000 ba
Jam’iyyar PDP, a wata sanarwa da mai magana da yawunta na kasa, Debo Ologunagba, ya fitar, ta zargi APC da shiga firgici da fargabar fuskantar babban zaben shugaban kasa a 2027.
A martanin APC, ta bayyana cewa PDP ce ke cikin rikici, kuma goyon bayan da Bola Ahmed Tinubu ke samu ya nuna cewa jama'a sun aminta da jagorancin Shugaban Kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

