Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Fadi Kuskuren Tinubu kan Zuwa Brazil

Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Fadi Kuskuren Tinubu kan Zuwa Brazil

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai wata ziyara ta kwanaki biyu zuwa kasar Brazil
  • Prince Adewole Adebayo wanda ya yi takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya nuna rashin gamsuwarsa kan ziyarar da Tinubu
  • Ya bayyana cewa ziyarar ba komai ba ce bata kudaden kasar nan domin abin da Tinubu ya je nema, akwai shi a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP a zaɓen 2023, Prince Adewole Adebayo, ya caccaki Shugaba Bola Tinubu.

Prince Adewole Adebayo ya caccaki Shugaba Tinubu ne kan ziyarar da ya kai zuwa kasar Brazil.

Adewole Adebayo ya caccaki Shugaba Tinubu
Hotunan Shugaba Bola Tinubu da Adewole Adebayo Hoto: @DOlusegun, @PrinceAdewole
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja a karshen mako.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An soki Shugaba Tinubu kan zuwa Brazil

Kara karanta wannan

2027: APC ta cika baki kan yiwuwar takara tsakanin Jonathan da Shugaba Tinubu

Ya bayyana ziyarar Shugaba Tinubu zuwa Brazil a matsayin ɓata kuɗaɗen kasa, inda ya ce babban bambancin kawai da ke tsakanin Najeriya da Brazil shi ne shugabanci.

Jigon na jam’iyyar SDP ya zargi Shugaba Tinubu da yin tafiya zuwa Brazil domin neman abin da yake yana cikin manufofin SDP.

Duk da haka, Prince Adewole Adebayo ya bayyana fatan cewa wannan ziyara za ta taimaka wa shugaban kasan ya fahimci yadda manufofin tattalin arzikinsa suke.

"Ziyarar ta yi kama da Saul ya zama Paul, domin abin da Brazil take da shi wanda Najeriya ba ta da shi shi ne shugabanci na gari.”
"Abin da suke da shi shi ne manufar rage talauci tare da shirye-shirye masu kyau. Idan ka dubi shirin Bolsa Familia, wanda ya rage talauci da kashi 27% a Brazil cikin shekara huɗu a karkashin gwamnatin Shugaba Lula da Silva, ya sabawa tsarin ‘an cire tallafi’ wanda ya kara talauci a Najeriya cikin sauri.”
"Idan ka kalli yadda ake tafiyar da Petrobras a Brazil, ka kwatanta da yadda Shugaba Tinubu yake tafiyar da NNPCL, bambancin na da matukar yawa."

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi gaskiyar abin da ke kai shi kasashen waje bayan dawowa daga Brazil

"Don haka, manufar tattalin arzikin Shugaba Tinubu ta sabawa wacce ta yi nasara a Brazil."
"Saboda haka, ina farin ciki cewa ya je can, domin ta hanyar zuwa can zai ga yadda manufofinsa suka kauce hanya."
"Amma, a gefe guda, ban yi farin cikin cewa ya kashe kuɗaɗe masu yawa wajen tafiyar. Da ya yi magana da ni, ko kuma ya duba manufar jam’iyyar SDP. Dama a baya ya kasance ɗan jam’iyyar SDP.”

- Prince Adewole Adebayo

Adewole Adebayo ya ragargaji Shugaba Tinubu
Hoton dan takarar shugaban kasa na SDP a zaben 2023, Adewole Adebayo Hoto: @PrinceAdewole
Source: Facebook

Tinubu ya kare kansa kan zuwa kasashen waje

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi martani kan masu ganin yawon gantali yake zuwa yi a kasashen waje.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa yana yin tafiye-tafiyen ne domin zakulo hanyoyin da zai samar da ayyukan yi da kawo ci gaba a kasar nan.

Mai girma shugaban kasan ya nuna cewa duk lokacin da ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya a kasar waje, ya yi hakan ne da nufin kawo ci gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng