Bayan Zargin Gwamna da Ƙoƙarin Tsige Shi, Kakakin Majalisa Ya Yi Murabus da Kansa
- Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Benue, Aondona Dajoh, ya ajiye mukaminsa a ranar Lahadi 24 ga watan Agustan 2026
- Hon. Dajoh ya tabbatar da murabus din nasa inda ya ce ya yi hakan ne domin mafita ga ci gaban jihar
- Dama dai majalisar ta dakatar da wasu ‘yan majalisa hudu saboda yunkurin tsige shi, amma Gwamna Hyacinth Alia ya musanta hannu a lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Benue, Aondona Dajoh, ya yi murabus daga mukaminsa.
Hon. Dajoh ya tabbatar da murabus din nasa inda ya ce ya yi haka ne saboda ci gaban jihar da samun zaman lafiya.

Source: Facebook
Kakakin majalisa ya yi murabus daga mukaminsa
Murabus ɗin nasa na cikin wasiƙa da ya sanya hannu ranar 24 ga Agustan 2025, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Kara karanta wannan
'Yan Majalisa da Sanatoci 50 da suka dumama kujera, ba su da gudumuwa a shekara 1
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wasiƙar, Hon. Dajoh ya ce:
“Na rubuto in yi murabus daga mukamin Kakakin Majalisa.”
“Na yi hakan da zuciya ɗaya kuma domin maslahar jihar, nagode wa abokan aiki bisa wannan damar.”
“Ina nan a shirye da cikakken sadaukarwa wajen ci gaba da aikina a matsayin ɗan majalisa na mazanar Gboko ta Yamma.”
Yadda aka dakatar da wasu yan majalisa
A ranar Juma’ar da ta gabata, majalisar ta dakatar da wasu mambobi hudu, Alfred Berger, Terna Shimawua, Cyril Ekong da James Umoru, na tsawon watanni shida.
Wannan hukuncin ya biyo bayan yunƙurin tsige Kakakin a daren da ya gabata wanda ya jawo matsala a jihar..
Shugaban masu rinjaye, Saater Tiseer, ya nemi a hukunta waɗannan ‘yan majalisar, cewar Punch.
Bayan haka, Dajoh ya umurci jami’an tsaron majalisar da su fitar da su daga zauren majalisa sannan ya nada Audu Elias a matsayin sabon mai magana.
Sai dai Gwamna Hyacinth Alia ya musanta cewa yana da hannu a yunƙurin tsige Kakakin. Ya ce yana da kyakkyawar dangantaka da majalisar.
Sakataren yada labaran Gwamna, Tersoo Kula, ya bayyana cewa:
“Gwamna Hyacinth Alia ba shi da hannu a kowane yunƙurin cire Kakakin ko wasu harkokin cikin majalisa.”

Source: Twitter
An zabi sunayen kwamishinoni a Benue
Kafin wannan, majalisar ta tabbatar da wasu sunaye shida a matsayin kwamishinoni, amma ta yi watsi da na Timothy Ornguga saboda korafe-korafe guda hudu.
Farfesan shari’a, Ornguga, ya fuskanci tambayoyi daga Manger Manger, ɗan majalisa mai wakiltar Tarka, kan ingancin takardun karatunsa da kuma takardar makaranta.
Majalisar ta bukaci Gwamna Alia ya maye gurbin Ornguga da James Dwen saboda gazawar su wajen kawar da zarge-zargen da aka shigar da su a kansu.
Hadimar gwamna ta bar duniya
Kun ji cewa Gwamnatin Benue ta gabbatar da rasuwar babbar mai ba gwamna shawara kan harkokin hulda da jama'a da siyasa, Mary Yisa.
Sakataren gwamnatin jihar, Serumun Aber ya ce mutuwar hadimar gwamnan kwatsam ya jefa abokan aikinta da dangi cikin bakin ciki.
Ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayiya Mary Yisa da yan uwanta, tare da addu'ar Allah sa ta huta har abada.
Asali: Legit.ng
