"Kan Mage Ya Waye": Jam'iyyar PDP Ta Kada Hantar APC, Ta Fadi Abin da Zai Faru a 2027

"Kan Mage Ya Waye": Jam'iyyar PDP Ta Kada Hantar APC, Ta Fadi Abin da Zai Faru a 2027

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta hango abin da zai faru a a lokacin zaben shekarar 2027 da ake tunkara
  • Mai magana da yawun jam'iyyar PDP ya zargi APC da jefa 'yan Najeriya cikin halin yunwa, talauci da rashin tsaro
  • Debo Olugunagba ya nuna 'yan Najeriya sun yi wayon da ba za su yarda su sake maida APC kan madafun iko ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta hango abin da zai faru a lokacin zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa zaɓen shekarar 2027 zai kasance kuri’ar raba-gardama kan yunwa, wahala da rashin tsaro da ake fuskanta a karkashin mulkin jam’iyyar APC mai ci.

PDP ta yi magana kan zaben 2027
Shugaban PDP na kasa, Umar Damagum da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @OfficialPDPNig, @DOlusegun
Source: Twitter

Mai magana da yawun PDP, Debo Ologunagba, ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ranar Talata a Abuja, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

Jihohi 3 da 'yan adawa suka lallasa APC a zaben cike gurbi a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP: 'Yan Najeriya ba za su zabi APC ba

Ya bayyana cewa ’yan Najeriya sun zama masu wayewa, kuma ba za su sake maido da APC kan mulki ba a zaɓen 2027.

’Yan Najeriya sun yi wayau a yanzu; abin da zai kasance a kan takardar kada kuri’a a 2027 shi ne yunwa, rashin tsaro da kuma rashin tabbas, abubuwan da babu kuɗin da za su iya saya.”

- Debo Ologunagba

Debo Ologunagba ya zargi APC da yin amfani da talauci a matsayin makami tare da tsananta matsalar tattalin arzikin a kasar nan, rahoton TheCable ya tabbatar.

Ya jaddada cewa wahalhalun da ’yan kasa ke fuskanta za su zama babban abin da zai zama manuniya a zaɓen 2027.

"Lokacin da PDP ke mulki, manoma suna amfani da wayar hannu wajen samun taki, a karkashin APC, ’yan Najeriya an tilasta musu sayan yunwa. A 2027, jama’a za su yi magana da murya ɗaya."

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa APC ta lashe mafi yawan zabukan cike gurbi da aka yi a Kano da jihohi 12'

- Debo Olugunagba

Jam'iyyar PDP ta nuna yatsa ga APC

Ya kuma yi zargin cewa APC ta yi amfani da jami’an tsaro wajen tsoratar da ’yan PDP a yayin zaɓen cike-gurbi da aka gudanar a jihohin Kaduna da Taraba a karshen mako.

Jam'iyyar PDP ta caccaki APC
Shugaban PDP na kasa, Umar Iliya Damagum, a wajen wani taron jam'iyyar Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter
"Amma akwai mummunan labari ga APC. Abin da ya faru a zaɓen cike-gurbin nan da suka kira zaɓe, ba zai sake faruwa a 2027 ba."
"Dalilin kuwa shi ne ’yan Najeriya sun yi wayo. Sun shiga cikin wahala. Abin da zai kasance a kan takardar kuri’a a 2027 shi ne yunwa, rashin tabbas da rashin tsaro, abubuwan da babu kuɗin da za su iya saya."

- Debo Olugunagba

PDP ta koka da zaben Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP reshen jihar Zamfara, ta yi fatali da zaben cike gurbi da aka gudanar a mazabar Kauran Namoda ta Kudu.

Ta zargi APC da yin amfani da sojoji da 'yan bindiga domin tafka magudi a zaben wanda aka gudanar a ranar Asabar.

Shugaban PDP na jihar Zamfara ya yi zargin cewa APC ta yi magudi a zaben tare da razana masu kada kuri'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng