Wasu Jagororin APC 3 Sun Tabbatar da Aniyar Neman Kujerar Shugaban Jam’iyya

Wasu Jagororin APC 3 Sun Tabbatar da Aniyar Neman Kujerar Shugaban Jam’iyya

Har yanzu ana ci gaba da hasashe game da wanda zai gaji Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Zuwa yanzu, akalla shugabannin APC uku sun tabbatar da cewa suna sha’awar zama shugaban jam’iyya a matakin kasa kafin babban zaben 2027.

Kafin yanzu, magoya bayan shugabanni a PDP da suka hada da na Tanko Al-Makura, Sakataren gwamnatin Najeriya, George Akume da Shugaban APC na riko na kasa, Ali Bukar Dalori na son a nada nasu a matsayin shugaban APC.

Jagororin APC sun fara nuna sha'awar kujerar shugaban jam'iyya
Mutum a APC sun bayyana bukatarsu ta jagorantar APC Hoto: Dr. Banks Ruh'Allah Omale/Engr Abubakar Iliyasu Haruna
Source: Facebook

A tattaunawarsu da Leadership, kowanne daga cikin jagororin sun bayyana dalilinsu na ganin sun cancanci kujerar shugabancin APC na matakin kasa.

Daga cikin dalilan da suka bayar, suna ganin da su aka kafa APC, kuma suna sane da matsalolinta da yadda za su taka rawa wajen kawo karshen rashin hadin kai a tsakanin 'ya'yanta.

Kara karanta wannan

APC: 'Yan siyasar Arewa sun fara neman kujerar Ganduje gadan gadan

Wadanda suka nuna sha'awarsu ta zama shugaban APC sun hada da:

Al-Makura na neman shugabancin APC

Tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma tsohon Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Kudu, Umaru Tanko Al-Makura, ya tabbatar da cewa yana son zama shugaban APC.

Al-Makura ya bayyana cewa kujerar shugabancin jam’iyya ta dace da wanda ke da masaniya da tarihin yadda aka hada jam’iyyar har ta yi tasiri a Najeriya.

Ya ce:

“Ba na gudanar da kamfe ko neman goyon baya a hukumance domin hakan zai sabawa dokar jam’iyya. Amma ina da kishin jagorantar wannan jam’iyya idan aka ba ni dama.”

Ya kuma jaddada cewa kasancewarsa daya daga cikin wadanda suka kafa APC, ya fahimci akidar jam’iyyar, hangen nesanta da manufofinta, .

Tsohon gwamnan Filato na son shugabancin APC

Haka zalika, tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye, ya tabbatar da cewa yana cikin wadanda ke neman kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Tsohon gwamnan Filato, Dariye da Abdullahi Ganduje
Dariye na sha'awar zama shugaban APC Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

Ya ce tuni ya fara tuntubar manyan shugabannin jam’iyyar a matakai daban-daban, yana mai cewa:

Kara karanta wannan

ADC ta yi martani ga fadar shugaban kasa, ta ce ta gama gigita APC

“Ni mai hada kan jama’a ne. Ba na cewa ni ne mafi cancanta, amma idan aka ba ni dama, zai zama girmamawa a gare ni na yi wa jam’iyya hidima. Zan taimaka wajen hada kan 'ya'yanta a sassa daban-daban na kasar nan."

Dariye ya sha alwashin hada kan 'yan APC domin tunkarar zaben 2027, yana mai cewa kasancewarsa tsohon gwamna da sanata ya jaddada cancantarsa.

Kailani: Zan farfado da jam’iyyar

A nasa bangaren, wani jigo a jam’iyyar APC, Farfesa Kailani Muhammad, ya ce yana ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki domin neman wannan kujera.

Game da abinda zai yi daban idan ya samu nasara, Kailani ya bayyana cewa:

“Zan farfado da jam’iyyar ta hanyar tabbatar da dimokuradiyya da samar da dama ga kowa da kuma yanayi mai kyau ga dukkannin ‘ya’yan jam’iyya.”

Ya kara da cewa zai mayar da gwamnatin jam’iyyar APC zuwa ga shugabanci nagari mai amfani ga al’umma.

Akume ya magantu kan neman shugabancin APC

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya nesanta kansa daga jita-jitar da ke yawo cewa yana daga cikin manyan ’yan siyasar da ke zawarcin kujerar shugabancin APC.

A cikin wata sanarwa, Akume ya ce:

Kara karanta wannan

Yadda jagororin APC suka ki tarbar Kashim Shettima a Kano bayan Ganduje ya yi murabus

“Gaskiyar magana, wannan zance ƙirƙirarsa kawai aka yi domin karkatar da hankali daga manyan ayyukan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dora min.”

Akume ya jaddada cewa ba zai taɓa cin amanar da shugaba Tinubu ya dora masa ba domin a ci gaba da aiwatar da ayykan ci gaban kasa.

Ya kara da cewa:

"Duk wani matsayi da na samu a rayuwata, Allah ne ya ba ni ta hannun mutane da suka haɗa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.”

'Yan APC sun kaure da rikici

A wani labarin, kun ji cewa Tsohuwar hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari Lauretta Onochie, ta magantu kan takarar tsohon shugaban Najeriya.

Lauretta Onochie ta zargi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da rashin mara wa Buhari baya lokacin da ya fito takarar shugabancin kasa a shekarar 2014.

Ta ce Tinubu bai da hannu a nasarar da Buhari ya samu wajen lashe zaben 2015, inda ta jaddada cewa lokacin ƙaryar da ake cewa Tinubu ne ya fito da Buhari ya ƙare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng