Ko Gezau: Minista Ya Fadi Fargabar Tinubu kan Batun Zaben 2027

Ko Gezau: Minista Ya Fadi Fargabar Tinubu kan Batun Zaben 2027

  • Ministan yaɗa labarai ya fito ya kare shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan surutun da ake yi dangane da zaɓen 2027
  • Mohammed Idris ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ba zai bari batun zaɓen ya kawar masa da hankali kan abin da ya sa a gaba ba
  • Ministan ya nuna cewa a cikin shekara biyu, gwamnatin Tinubu ta kawo muhimman sauye-sauye a ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya yi magana kan yunƙurin kifar da Shugaba Bola Tinubu da ƴan adawa ke yi a zaɓen 2027.

Mohammed Idris ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ba ya barin surutun da ake yi kan zaɓen shekarar 2027 ya kawar masa da hankali.

Tinubu ya maida hankali kan inganta Najeriya
Tinubu ba ya damuwa da batun zaben shekarar 2027 Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, a shafin X na ma'aikatar yaɗa labarai ta Najeriya.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya fadi damar da Atiku ya rasa ta zama shugaban kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu bai damu da batun zaɓen 2027 ba

Mohamed Idris ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana ci gaba da mai da hankali kacokan kan aikinsa na kawo sauye-sauyen da za su amfani ƙasa da haɓaka tattalin arzikin Najeriya yadda ya kamata.

Ministan ya bayyana cewa cikin shekaru biyu kacal da gwamnati ke kan mulki, burin nan na sauyi da cigaba ya fara haifar da ainihin sakamako a fili.

“Yayin da ake ci gaba da tattaunawa a fagen siyasa da kuma ƙaruwar jita-jita daga kafafen yaɗa labarai dangane da zaɓen 2027."
"Ya zama dole mu jaddada cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na nan daram da alƙawarin da ta ɗauka, wato kawo gyare-gyare masu amfani da kuma ci gaban tattalin arziki ga al’ummar Najeriya."
"Ko da yake muna jaddada ƴancin ƴan Najeriya na amfani da damar da kundin tsarin mulki ya ba su wajen haɗuwa da faɗin albarkacin baki, yana da muhimmanci mu fahimtar da jama’a cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ba za ta yarda ta ruɗe da maganganun siyasa marasa amfani ba."

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun kunyata haɗakarsu Atiku, sun hango wanda ya dace da Najeriya a 2027

“Surutun da ake yi a kafafen yaɗa labarai game da bayyanar wata sabuwar haɗaka abin fahimta ne, amma ya kamata a tuna cewa ƴan Najeriya sun ba Shugaba Tinubu amanar sauya lamurra a cikin tsarin ‘Renewed Hope’."
“Ba abin mamaki ba ne cewa waɗanda ke ƙoƙarin kafa sababbin ƙungiyoyin siyasa da haɗaka su na ƙoƙarin karkatar da hankalin mutane daga ci gaban da Najeriya ke samu."
"Amma wannan gwamnati ba za ta yarda da wani ɓata lokaci daga waɗanda suka fi son ƙin cigaba da canji ba."
“Gwamnatin Tinubu na nan daram, ba ta karkace ba, kuma tana da cikakken ƙuduri na gina Najeriya mai bunƙasa da alheri ga kowa da kowa.”

- Mohammed Idris

Mohammed Idris ya kare Shugaba Tinubu
Mohammed Idris ya ce Tinubu ya maida hankali kan kawo ci gaba a kasa Hoto: @FMINONigeria
Source: Twitter

Malami ya gargaɗi Tinubu kan tazarce

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban cocin INRI Evangelical, Primate Elijah Ayodele, ya aika saƙo ga Shugaba Bola Tinubu.

Primate Ayodele ya buƙaci shugaban ƙasan da ka da ya sanya a ransa cewa zai zarce kan mulkin Najeriya a wa'adi na biyu.

Malamin addinin na Kirista ya bayyana cewa haɗakar ƴan adawa da aka kafa, akwai wani ɓoyayyen lamari dangane da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng