Matsalolin da Peter Obi Zai Fuskanta idan Ya Samu Tikitin ADC

Matsalolin da Peter Obi Zai Fuskanta idan Ya Samu Tikitin ADC

FCT, Abuja - Peter Obi na da burin ganin ya hau kan kujerar shugabancin Najeriya a zaɓen shekarar 2027 da ake tunkara.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

A zaɓen shekarar 2023, Peter Obi ya jaraba sa'arsa wajen yin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar LP.

Peter Obi zai iya fuskantar matsaloli a zaben 2027
Akwai abubuwan da za su iya kawo cikas ga Peter Obi a zaben 2027 Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Peter Obi zai yi takara a 2027

A yayin wata hira da tashar Channels tv, Peter Obi ya bayyana aniyarsa ta sake yin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, jaridar The Punch ta ce kakakin Peter Obi, Ibrahim Umar ya bayyana cewa maigidansa bai da niyyar yin haɗakar takara da Atiku Abubakar.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya bayyana cewa yana ƙwarin gwiwar daidaita al'amuran ƙasar nan cikin shekara biyu a mulkinsa.

Waɗanne matsaloli Peter Obi zai iya fuskanta?

Peter Obi ya shiga cikin haɗakar ƴan adawa a ƙarƙashin jam'iyyar ADC domin kifar da Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

ADC ta ɓullo da sabon tsari, ta gindaya wa Atiku, Obi da Amaechi sharaɗin neman takara a 2027

Akwai matsaloli da dama da Peter Obi zai iya fuskanta idan ya samu tikitin ADC domin yin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Ga wasu daga cikinsu a nan ƙasa:

1. Yardar Arewa

Gagarumar matsala ta farko da Peter Obi zai fuskanta ita ce samun yardar yankin Arewacin Najeriya.

Peter Obi wanda ya fito daga yankin Kudu maso Gabashin Najeriya na iya fuskantar rashin samun goyon bayan yankin Arewa.

Ɗan ƙabilar Igbo bai taɓa shugabancin Najeriya a ƙarƙashin mulkin dimokuraɗiyya ba.

Wasu daga cikin mutanen Arewacin Najeriya na zargin Peter Obi da nuna sassauci ko goyon bayan ayyukan ƙungiyar IPOB.

Ko a baya-bayan nan, yayin wata hira da tashar Channels tv, Peter Obi ya soki cigaba da tsare shugaban IPOB, Nnamdi Kanu da gwamnatin tarayye ke yi.

Ƙungiyar IPOB ta yi ƙaurin suna wajen kai hare-hare kan jami'an tsaro da sauran mutane fararen hula musamman waɗanda suka fito daga Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

2027: ADC ta fadi shirinta kan masu burin takarar shugaban kasa

2. Addini

Batun addini zai iya kawo cikas ga burin Peter Obi na zama shugaban ƙasan Najeriya a zaɓen 2027.

Addini yana taka muhimmiyar rawa kan yadda ƴan Najeriya suke zaɓar shugabanninsu a lokutan zaɓe.

Zai zama abu mai matuƙar wahala yankin Arewa ya yarda ya rabu da tikitin Muslim-Muslim bayan shekara huɗu kacal domin goyon bayan Peter Obi wanda zai so ya yi shekara takwas a kan mulki.

3. Samun goyon bayan Atiku da sauran ƴan siyasa

Ba ɓoyayye abu ba ne cewa Atiku Abubakar yana da burin yin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 duk da har yanzu bai fito ya bayyana hakan ba.

Idan Peter Obi ya samu tikitin ADC, zai buƙaci samun goyon bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasan na Najeriya.

Bayan Atiku, Peter Obi zai buƙaci samun goyon bayan manyan ƴan siyasa irinsu Rotimi Amaechi da Nasir El-Rufai idan ya samu tikitin ADC.

Rotimi Amaechi dai na daga cikin ƴan siyasa daga Kudancin Najeriya da ke da niyyar yin takarar shugaban ƙasa a 2027.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar haɗaka ADC ta zaɓi ɗan takara tsakanin Atiku, Obi da Amaechi? An samu bayanai

Samun goyon baya da yardar waɗannan ƴan siyasan na daga cikin ƙalubalen da Peter Obi zai fuskanta wajen neman shugabancin Najeriya.

Peter Obi na son zama shugaban Najeriya a 2027
Peter Obi zai yi takarar shugaban kasa a 2027 Hoto: @PeterObi
Asali: Facebook

4. Ɗauko abokin takara

A zaɓen shekarar 2023, Peter Obi ya ɗauki Yusuf Datti Baba-Ahmed a matsayin abokin takararsa.

Samun abokin takara a zaɓen 2027, na daga cikin matsalolin da Peter zai fuskanta a zaɓen 2027.

Idan ya samu tikitin ADC, dole ne ya yi watsi da Yusuf Datti Baba-Ahmed wanda suka yi gwagwarmaya da faɗi tashi tare gabanin zaɓen 2023 da bayansa.

Ɗauko abokin takara daga Arewacin Najeriya ka iya zama ƙalubale ga Peter Obi domin bai da farin jini a wajen mutanen yankin musamman Musulmai.

Da wuya a samu wani gogaggen ɗan siyasa wanda yake da ƙarbuwa a yankin Arewacin Najeriya ya yarda ya zama abokin takarar Peter Obi a zaɓen 2027.

Peter Obi ya faɗi shirinsa kan Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Peter Obi ya bayyana tanadin da ya yi wa yankin Arewacin Najeriya idan ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

"Zai iya kifar da Tinubu," Momodu ya faɗi wanda ya dace ADC ta tsayar takara a 2027

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya bayyana cewa yana da mafita kan magance matsalar rashin tsaron da ta addabi yankin.

Ya bayyana cewa yankin Arewa zai yi murna idan har ya samu damar ɗarewa kan shugabancin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng