Saukar Ganduje daga Shugabancin APC Ya Bar Babban Giɓi a APC, An Sa Ranar Taron NEC
- Jam'iyyar APC mai mulki ta zaɓi ranar 24 ga watan Yuli, 2025 a matsayin ranar da za ta gudanar da taron kwamitin zartarwa (NEC)
- Mataimakin sakataren APC na ƙasa, Festus Fuanter ya ce a taron NEC ne za a zaɓi sabon cikakken shugaban jam'iyya na ƙasa
- Wannan dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga shugabancin APC, lamarin da ya ba mutane mamaki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - APC mai mulkin Najeriya ta sanya ranar 24 ga Yuli, 2025 domin gudanar da taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar.
Jam'iyyar APC ta tabbatar da cewa a wannan taron, za a zaɓi cikakken shugaban jam'iyya, wanda zai maye gurbin Dr. Abdullahi Umar Ganduje

Source: Twitter
APC ta gudanar da taron kwamitin NWC
Leadership ta tattaro cewa APC ta yanke wannan hukunci ne a taron kwamitin gudanarwa (NWC) wanda ya gudana ƙarƙashin shugaban riko, Ali Dalori.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan dai shi ne karo na farko da APC ta gudanar da taron NWC tun bayan saukar Abdullahi Ganduje daga matsayin shugaban jam'iyya na ƙasa.
Ali Dalori, mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa (Arewa), ya karɓi ragamar APC a matsayin shugabanta na riko, bayan murabus da Dr. Ganduje ya yi.
An fara shirin lalubo shugaban APC na ƙasa
Yayin da yake jawabi ga manema labarai, mataimakin sakataren jam’iyyar, Festus Fuanter, ya ce taron NEC zai bai wa jam’iyya damar zaɓar sabon shugaban APC na ƙasa.
Fuanter ya bayyana cewa an riga an aike da takardar sanarwa ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) dangane da shirin gudanar da taron NEC.
“Duk abin da muke yi yanzu, har da tabbatar da mukaddashin shugaban jam’iyya, sai an samu amincewar NEC.
"Idan a lokacin taron NEC aka zaɓi sabon shugaban jam’iyya, za mu karɓe shi sannan mu jira babban taron jam’iyya wanda za a zaɓi sababbin shugabanni,” in ji Faunter.

Kara karanta wannan
'Ganduje ya jawo wa Kano abin kunya,' NNPP ta yi magana kan komawar Kwankwaso APC

Source: Twitter
Abubuwan da APC ta tattauna a taron NWC
Ya kara da cewa APC ta tattauna kan batun shirin gudanar da zaɓukan cike gurbi a wasu jihohi wanda hukumar INEC ta shirya gudanarwa, rahoton Premium Times.
Haka kuma ya bayyana cewa NEC a matsayin majalisar ƙoli mai ikon yanke shawara kan abubuwan da suka shafi jam'iyya a cikin gida.
A cewarsa, NEC zai tattauna kan muhimman batutuwa a taro mai zuwa, ciki har da zaɓen sababbin shugabanni, sake fasalin cikin gida, da kuma shirin jam’iyyar na tunkarar babban zaɓen 2027.
Maryam Shetty ta yi magana kan saukar Ganduje
A wani labarin, kun ji cewa Maryam Shettima, wacce aka fi sani da Maryam Shetty ta ce murabus ɗin Abdullahi Umar Ganduje bai ba ta mamaki ba.
Dr. Maryam Shetty ta ce dama a duniya, komai yana da farko kuma yana da karshe, Allah ƙaɗai ne ba Shi da ƙarshe.
A cewarta, tsohon gwamnan Kano ya jima yana shugabantar APC kuma dama an saba ganin yadda shugabannin jam'iyyar ke ƙarewa da rikici.
Asali: Legit.ng
