Kawu Sumaila Ya Tabo Batun Komawarsa APC, Ya Bayyana Shirin da Yake Yi a Kano

Kawu Sumaila Ya Tabo Batun Komawarsa APC, Ya Bayyana Shirin da Yake Yi a Kano

  • Sanata mai wakiltar mazaɓar Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila ya bayyana matsayarsa kan kiran da shugabannin APC suka yi masa
  • Kawu Sumaila ya bayyana cewa ya fara neman shawarwari daga mutanen mazaɓarsa domin yanke shawara game da komawa jam'iyyar APC
  • Sanatan na jam'iyyar NNPP ya bayyana cewa duk abin da mutanen mazaɓarsa suka yanke, to da shi zai yi amfani a matsayin makomarsa a siyasa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya yi magana kan kiran da shugabanni APC suka yi masa na ya koma jam'iyyar.

Sanata Kawu Sumaila ya bayyana cewa fara tuntuɓar mutanen mazabarsa domin yanke shawarar ko ya kamata ya koma APC, bayan kiraye-kirayen da jagororin jam’iyyar daga yankin Sanatan Kano ta Kudu suka yi masa.

Kawu Sumaila
Kawu Sumaila ya fara neman shawarwari kan komawa APC Hoto: Abdulrahman Kawu Sumaila
Asali: Twitter

An buƙaci Kawu Sumaila ya koma APC

Kara karanta wannan

Sanata Ndume bai gaji ba, ya sake ba Shugaba Tinubu muhimmiyar shawara

Jaridar Daily Trust ta ce yayin da yake mayar da martani kan wannan kira, Kawu Sumaila ya ce ya fara neman shawarwari daga mutanen mazaɓarsa da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin APC na ƙananan hukumomi 16 da sakatarorinsu daga Kano ta Kudu sun yi kira ga sanatan da ya koma jam’iyyar.

Da yake magana a madadinsu, shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Albasu, Alhaji Iliya Jibrin Hungu, ya ce dawowar Sumaila za ta ƙarfafa jam’iyyar domin samun nasara a zaɓuka masu zuwa.

Me Kawu Sumaila ya ce kan dawowa APC?

“Gaskiya ne cewa shugabannin APC daga mazaɓata sun roƙe ni da na koma jam’iyyar APC. Jagororin sun yi amfani da rikicin cikin gida da ke cikin jam’iyyata ta NNPP, wanda ya raba jam’iyyar gida biyu."
“Kuma na tabbata suna kallon ƙarfina ne a siyasance, da kuma jajircewata a cikin harkar siyasa. Don haka, da kiraye-kirayen suka fara yawa, na fara tuntubar al’ummata da duk masu ruwa da tsaki.”

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: APC ta bukaci Ganduje ya taya ta kwato Kawu Sumaila daga NNPP

“Na shiga siyasa ne saboda mutanena, kuma duk wani hali da na tsinci kaina a ciki, ina bari su yanke min hukunci. Haka ma wannan batun, ba zan yanke hukunci da kaina ba, zan bari su yanke hukunci."
“Duk hukuncin da al’ummata suka yanke, zan bi shi, domin a siyasa, neman shawara da fayyace gaskiya suna da matuƙar muhimmanci."
"Don haka, abu ɗaya da zan bayar da tabbaci a kai shi ne, ba zan yanke hukunci ni kaɗai ba, kuma duk abin da al’ummata suka yanke, zan bi."

- Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila

Kawu Sumaila
Kawu Sumaila ya fara shawara kan komawa APC Hoto: Abdulrahman Kawu Sumaila
Asali: Twitter

A ranar Talata dai, shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya sanya labule tare da Sanata Kawu Sumaila da wasu jiga-jigan jam'iyyar NNPP.

NNPP ta dakatar da Sanata Kawu Sumaila

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano ta dakatar da wasu daga cikin ƴan majalisunta.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar wakilai ya bayyana halascin da Tinubu ya yi masa a siyasance

Jam'iyyar NNPP ta dakatar da sanata mai wakiltar Ƙano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila da wasu ƴan majalisar wakilai guda uku.

Shugaban NNPP na jihar Kano, Hashimu Dungurawa ya bayyana cewa an dakatar da ƴan majalisar ne bisa zargin cin amanar jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng