Sabuwar Rigima Ta Ɓarke a PDP, Gwamnoni 5 Sun Fara Tunanin Ficewa daga Jam'iyya

Sabuwar Rigima Ta Ɓarke a PDP, Gwamnoni 5 Sun Fara Tunanin Ficewa daga Jam'iyya

  • Alamu sun nuna sabuwar rigima ta ɓalle a tsakanin gwamnonin PDP da shugabanni jam'iyyar na kasa
  • An ruwaito cewa akalla gwamnoni biyar daga cikin 12 tare da wasu jiga-jigai sun fara tunanin barin PDP zuwa APC ko haɗakar da ake shirin yi kafin 2027
  • Wani shugaba a PDP ya ce yanzu gwamnoni sun daina ba jam'iyyar gudummuwar kudi domin tafiyar da harkokinta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Babban jam’iyyar adawa a Najeriya (PDP) na fuskantar sabon rikici a cikin gida wanda ke kara jefa makomar jam’iyyar cikin duhu, shekaru biyu bayan shan kaye a 2023.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnoni 12 na PDP sun fara nesanta kansu daga shugabancin jam’iyyar na kasa, lamarin da ke haifar da shakku game da yiwuwar gudanar da taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) a watan Mayu.

Kara karanta wannan

Abin ya fara damun Tinubu, an 'gano' shirinsa kan ƴan APC da ke son komawa SDP

Gwamnonin PDP.
Baraka ta kunno kai a tsakanin gwammonin PDP 12 Hoto: @SenBalaMuhammed
Asali: Twitter

Gwamnonin PDP 5 sun fara tunanin sauya sheka

Wasu majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun shaida wa Tribune Online cewa akalla gwamnoni biyar sun fara tunanin barin PDP zuwa APC ko su bi haɗakar da ake shirin yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan rikici na cikin gida na da nasaba da tasirin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike da kuma abokan tafiyarsa a kwamitin gudanarwa na PDP (NWC).

A cikin gwamnonin PDP 12, gwamna daya tilo ne ya bayyana matsayarsa kan rikicin kujerar sakataren PDP tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Udeh-Okoye.

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ne kaɗai ya goyi bayan Sunday Udeh-Okoye a matsayin Sakataren Jam’iyya na kasa, sabanin Sanata Samuel Anyanwu wanda ke ikirarin kujerar.

Sai dai har yanzu ba a san takamaiman matsayin dangantakar Makinde da Wike ba, musamman ganin irin hadin kan da suka yi a tsohuwar kungiyar G5 da ta yi adawa da PDP a 2023.

Kara karanta wannan

Atiku, El Rufai, Malami da sauran manyan ƴan adawa da suka ziyarci Buhari a Kaduna

Wane rikici ya sake ɓarkewa a PDP?

Cikin watanni da dama, an lura cewa gwamnonin PDP sun daina ziyartar hedkwatar jam’iyyar ta ƙasa da ke a Abuja, kuma ayyukan jam’iyyar sun ragu matuka.

Jam’iyyar da ke dogara da gudunmawar kuɗi daga gwamnoni wajen gudanar da ayyukanta, yanzu tana rayuwa ne bisa taimakon wasu jiga-jigai masu hannu da shuni.

Jam'iyyar PDP.
Gwamnoni sun janye tallafin da suka ba jam'iyyar PDP Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

An tattaro cewa a yanzu gwamnoni sun dakatar da bada kudaden tafiyar da harkokin PDP saboda ba su jin daɗin abin da ke faruwa, rahoton Guardian.

Wani mamban NWC da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce:

“Gwamnoni sun daina ba mu kudi don tafiyar da jam’iyya, amma muna kokari. Babu dalilin da zai hana jam’iyya ta ci gaba da rayuwa, ya kamata gwamnoni su duba.”

PDP ta gaza ɗaukar mataki kan Wike

Wani mamba a NWC ya ce kwamitin ya rasa kataɓus, musamman idan lamarin ya shafi Wike.

Ya ce:

Kara karanta wannan

CPC: Ana hasashen ficewar mutanen tsohon shugaban kasa Buhari daga APC

"Wike ya aikata duk abin da ya sabawa jam’iyya, amma ba za mu iya masa komai ba. Ka tambayi Damagum, ka tambayi Anyanwu.”

Wani shugaba a PDP ta jihar Katsina, ya ce matsalar jam'iyyar a fili take idan har da gaske ana son farfaɗo da jam'iyyar dole sai an rufe ido an ɗauki mataki mai tsauri.

Da yake zantawa da wakilin Legit Hausa bisa sharadin sakaya sunansa, ya ce shugabannin PDP na ƙasa sun san inda matsalar take amma sun gaza ɗaukar mataki.

"Na daina damuwa da rigingimun PDP, wallahi ka ji na rantse maka shugabannin mu sun san su waye matsalar, sun san bara gurbin amma har yau an gaza ɗaukar mataki a kansu.
"Babu ta yadda za a warware waɗannan matsalolin ba tare an taka wa wasu burki ba, an san komai kuma an san yadda za a warware amma ba za a yi ba ne," in ji shi.

Kara karanta wannan

Atiku, Obi da El Rufai na shirin haɗewa, Tinubu ya bude kofar kayar da shi a 2027

Kakakin PDP a Ondo ya yi murabus

A wani labarin, kun ji cewa kakakin PDP reshen jihar Ondo, Kennedy Peretei, ya yi murabus daga muƙaminsa kuma ya tattara ya bar jam'iyyar.

A wasiƙar da ya rubuta, tsohon mai magana da yawun PDP ya caccaki shugabannin jam’iyyar da rashin cancanta da gazawa wajen jagoranci yadda ya kamata.

A cewarsa, shugabanni da wasu jiga-jigan PDP a jihar Ondo ba su da niyya ko shirin lashe kowanne irin zaɓe, neman kudi kawai suke yi da jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262