Peter Obi Ya Gama Magana,Ya Fadi Matsayarsa kan Ficewa daga Jam'iyyar LP

Peter Obi Ya Gama Magana,Ya Fadi Matsayarsa kan Ficewa daga Jam'iyyar LP

  • Peter Obi wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya yi magana kan jita-jitar da ke cewa yana shirin barin jam'iyyar LP
  • Tsohon gwamnan na jihar Anambra, ya bayyana cewa ƙarya ake yi masa domin bai taɓa yin irin wannan maganar da kowa ba
  • Peter Obi ya kuma yi kira ga mambobin LP da ka da su ji tsoron yin magana idan sun ga abubuwa ba su tafiya daidai a ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen shekarar 2023, Peter Obi, ya ƙaryata jita-jitar da ke cewa yana shirin barin jam’iyyar.

Peter Obi ya bayyana cewa bai yi wata tattaunawa da kowane mutum ko wata ƙungiya ba dangane da barin jam'iyyar LP.

Kara karanta wannan

"Mutum 1 ke juya APC," Tsohon mataimakin shugaban PDP ya faɗi shirin da suke yi

Peter Obi
Peter Obi ya ce bai da shirin ficewa jam'iyyar LP Hoto: Mr. Peter Obi
Asali: UGC

Peter Obi ga bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar a taron ƙwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) da ke gudana a Abuja, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi ya taɓo batun ficewa daga LP

Ya jaddada cewa duk wani yanke hukunci da ya shafi makomar jam’iyyar za a cimma sa ne ta hanyar tuntuɓar dukkan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar

“Ban taɓa faɗawa kowa cewa zan bar jam'iyyar LP ba."

- Peter Obi

Peter Obi ya buƙaci mambobin jam’iyyar da kada su ji tsoron kowa, yana mai jaddada cewa Najeriya ta kama hanyar durkushewa, kuma tana buƙatar ceto cikin gaggawa.

Wace shawara Peter Obi ya ba mambobin LP?

“Ka da ku ji tsoron kowa. Waɗanda suka ji tsoro a baya ba su yi wani abin a zo a gani ba."
“Dole ne mu riƙa magana idan abubuwa suna tafiya ba daidai ba. Najeriya na durƙushewa. Bayanai sun nuna cewa mutane na ƙara talaucewa a kullum."

Kara karanta wannan

An fayyace shirin Peter Obi na 'hadewa' da El Rufai a jam'iyyar SDP

- Peter Obi

Ya jaddada bukatar haɗin kai da tafiya da kowa a cikin jam’iyyar.

Peter Obi
Peter Obi ya ce bai da shirin ficewa daga LP Hoto: @peterobi
Asali: Twitter
“LP ta zaɓi zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, kuma dole ne mu gudanar da komai a matsayin ƴan uwa."
"Ba ra'ayin Peter Obi ba ne kaɗai, ra'ayin kowa ne. Wannan ƴan uwantakar ba ta barin kowa a baya. Muna son gina jam’iyya mai adalci da gaskiya."
“Muna son shiga zaɓe na gaba cikin shiri, za mu ba ƴan Najeriya ƴan takara mafi nagarta da cancanta daga majalisar wakilai, majalisar dattawa, gwamnoni, har ma da shugaban ƙasa."

- Peter Obi

Peter Obi ya magantu kan janye gayyatar Sanusi II

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi magana kan janye gayyatar da ƴan sanda suka yi wa Muhammadu Sanusi II.

Peter Obi ya nuna jin daɗinsa kan matakin da shugaban ƴan sandan Najeriya ya ɗauka na janye gayyatar da aka yi wa sarkin Kano na 16 zuwa birnin tarayya Abuja.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana cewa gayyatar da aka yi wa sarkin na iya tayar da hankulan jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng