Atiku, Obi da El Rufai na Shirin Haɗewa, Tinubu Ya Bude Kofar Kayar da Shi a 2027

Atiku, Obi da El Rufai na Shirin Haɗewa, Tinubu Ya Bude Kofar Kayar da Shi a 2027

  • Jagoran jam’iyyar SDP, Prince Adewole Adebayo, ya ce Bola Tinubu yana yin abubuwan da za su kai ga faduwar jam’iyyarsa ta APC a 2027
  • Adebayo ya zargi gwamnatin APC da kassara rayuwar 'yan Najeriya tare da kashe tiriliyan a kan ayyuka da ba su da amfani ko amfani da jama’a
  • Ya ce SDP na neman hadin kan jama’a maimakon hadin gwiwar 'yan siyasa, domin hakan ne zai taimaka wajen kayar da APC da Tinubu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jagoran jam'iyyar SDP, Prince Adewole Adebayo, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya bude kofar da za a kayar da shi a zaben 2027.

Prince Adebayo, wanda tsohon dan takarar shugaban kasa ne, ya ce yanzu Tinubu yana yin abubuwan da za su jawo faduwar jam'iyyarsa ta APC cikin sauki.

Kara karanta wannan

"Mutum 1 ke juya APC," Tsohon mataimakin shugaban PDP ya faɗi shirin da suke yi

Jagoran SDP ya magantu kan nasarar jam'iyyar a zaben 2027
Jagoran SDP ya hango yadda jam'iyyar za ta kayar da Tinubu da APC a zaben 2027. Hoto: @officialsdp1, @officialABAT
Asali: Facebook

'Dan takaran SDP ya magantu kan nasarar jam'iyyar

A wani rahoton Leadership, Prince Adebayo ya yi shagube da cewa Tinubu ya dauko hanyar zama shugaban kasa na karshe da APC za ta yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon dan takarar shugaban kasar na SDP ya ce:

“Mutanen da ke fafutukar ganin SDP ta karbi mulki suna cikin gwamnatin APC tsumu tsumu, domin sun san cewa sun kunna wuta a bayan 'yan Najeriya, suna neman mafita
"Sun sanya rayuwa ta yi wuya ga 'yan Najeriya tare da yanke shawarwarin da ba su amfanar jama'a. Suna kashe tiriliyoyin kudi kan ayyukan da ba a iya gani a zahiri."

'Tinubu yana aiki don nasarar SDP a 2027' - Adebayo

Prince Adewole Adebayo ya kara da cewa:

"An gabatar da kasafin N5trn wanda ba zai amfani mutane ba. Saboda haka, Shugaba Tinubu yana aiki tukuru ne kawai don mu zo mu doke shi daga mulki.
"Yana aiki tukuru don ganin cewa shi ne shugaban kasa na karshe da APC za ta yi. Duk abin da su ke yi, zai zo ya zame masu ala-kai-kai, don mutane ba su mori gwamnatinsu ba."

Kara karanta wannan

APC na ragargazar 'yan adawa a Kano, Barau ya karbi shugabannin jam'iyyar hamayya

Da aka tunatar da shi cewa jam'iyyarsa ba ta da tsarin da zai doke Tinubu da APC, ya amince cewa ba lallai ne SDP tana da tsari mai kyau yanzu ba, amma tana da yakinin cewaa mutane za su zabe ta.

Jaridar Tribune ta rahoton tsohon dan takarar shugaban kasar yana cewa:

“Mu ba mu da wani tarihi na aikata laifi, cin hanci ko rashawa, ko kuma karkatar da kudaden jama'a, don haka mun dogara ne da tasirin mutane.”

SDP ta yi magana kan hada kai da 'yan adawa

Adewole Adebayo ya yi magana kan yiwuwar hadewar SDP da jam'iyyun adawa
Adewole Adebayo ya ce babu wani amfani a hadakar jam'iyyun adawa. Hoto: @Pres_Adebayo
Asali: Facebook

A martani ga zancen cewa zai yi wuya a doke Tinubu ba tare da hadin gwiwar 'yan adawa ba, Prince Adebayo ya yi ikirarin cewa:

“Duk wata hadaka da ba za ta amfani jama'a ba, ba za ta yi tasiri ba. Abin da muke so mu yi yanzu shi ne neman hadin kan 'yan Najeriya. Ba a taɓa gwada hakan ba, saboda abin da APC ta gwada wanda ya samar da Shugaba Muhammadu Buhari shi ne majar 'yan siyasa.

Kara karanta wannan

Ana rade radin Tinubu ya tsige shi, Mahmud Yakubu ya saka labule da ma'aikatan INEC

“Kuma da wannan ne muke da fahimtar cewa hadewar 'yan siyasa ba zai burge kowa a yanzu ba, an gwada a baya, amma a karhe aka gane sun hade ne don muradun kansu ba na jama'a ba.
“Zan iya tabbatar muku cewa da zarar mun fito da mufofinmu, kuma muka nemi hadin kan jama'a, to za mu yi wa Shugaba Tinubu ritaya daga siyasa a wa'adin farko."

SDP ta ja kunnen El-Rufai da sauransu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugabannin SDP sun yi gargaɗi ga Mallam Nasir El-Rufai, da sauran sababbin mambobi da su mutunta tsarin jam’iyyar.

Shugaban SDP na Legas, Femi Olaniyi, ya bayyana cewa jam’iyyar ba za ta sauya kundin tsarin mulkinta, tambari ko taken ta don faranta ran kowa ba.

Ya kuma bukaci sababbin mambobi da su bi doka ta hanyar yin rajista a matakin gunduma, tare da gujewa duk wani mataki da zai karya tsarin cikin gida na jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.