Gwamna Ya Ciri Tuta, Jam'iyyar APC Ta ba Shi Tikitin Takara a Zaɓen 2027
- Jam'iyyar APC ta bai wa Gwamna Bassey Otu na jihar Kuros Ribas tikitin neman tazarce ba tare da hamayya ba a zaɓen 2027
- Shugaban APC, Alphonsus Eba ya ce sun gamsu da shugabancin Otu don haka ba za su yi kuskuren sauka daga jirgin nasara ba
- Eba ya yi kira ga sauran ƴan APC da ke da burin neman takara a zaɓe mai zuwa da su fara tuntuɓa da neman shawarwari tun yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Cross River - Jam’iyyar APC reshen jihar Kuros Riba ta bai wa Gwamna Bassey Otu da mataimakinsa, Peter Odey, tikitin takara babu hamayya a zaben 2027.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kuros Riba, Alphonsus Eba, ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a hedikwatar APC da ke Kalaba.

Asali: Twitter
Eba ya bukaci sauran mambobin APC da ke da sha’awar neman mukaman siyasa da su fara tuntuba, neman shawara da shirin takara tun yanzu, rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Bassey Otu kaɗai APC ta ba tikiti
Shugaban jam'iyya mai mulki ya jaddada cewa ba wanda aka bai wa tikitin takara sai gwamna da mataimakinsa.
Ya kuma shawarci masu sha’awar takarar su koma mazabunsu domin samun goyon baya daga al’ummarsu.
“Kwamitin gudanarwa na jiha da kwamitin zartarwa sun gana a yau kuma sun yanke shawarar cewa Gwamna Otu ne kadai zai tsaya takarar APC a 2027,” in ji Eba.
Me yasa APC ta ba gwamnan tikitin 2027?
Mista Eba ya ƙara da cewa sun ɗauki wannan matakin ne saboda babu mai hankalin da zai canza tawagar nasara.
Bugu da ƙari, Eba ya ce ko da Gwamna Otu bai nuna sha’awar sake tsayawar gwamna ba, jam'iyyar APC za ta ci gaba da mara masa baya, kamar yadda ta yi a 2022.

Kara karanta wannan
A karon farko, gwamna Fubara ya fadi halin da ya shiga bayan dokar ta baci a Ribas
“Muna rokon shi (Mai girma Gwamna Otu) da ya saurari bukatar ‘yan jam’iyya kuma ya amince da wannan zabin,” in ji shi.
Eba ya yabawa mataimakin gwamna, Peter Odey, wanda ke rike da kujerar muƙaddashin gwamna a halin yanzu.

Asali: Getty Images
APC ta jinjinawa muƙaddashin gwamna
Ya yabe shi ne bisa goyon bayansa ga matakan da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya dauka a rikicin siyasar jihar Ribas.
Ya bayyana cewa wasu mutane sun yi kokarin bata matsayar jihar Kuros Riba game da rikicin jihar Ribas da matakan da Tinubu ya ɗauka ciki har da dokar ta ɓaci
Amma a cewarsa, Odey ya fito ya fayyace cewa gwamnonin Kudu maso Kudu ba su tuntube shi ba kafin su soki matakin Tinubu.
Har ila yau, ya jinjinawa Shugaba Tinubu bisa kokarinsa na dawo da zaman lafiya a jihar Ribas, wanda ya hana rikicin siyasa yin kamari, rahoton Punch.
Gwamna Otu ya dakatar da hakimi

Kara karanta wannan
"Hantar Tinubu ta kaɗa": An faɗi wanda ya dace Atiku, Obi da El Rufai su marawa baya a 2027
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Bassey Otu na jihar Kuros Riba ya dakatar da Hakimin Esuk Utan, Cif Okon Archibong, tare da ƴan Majalisar masarautarsa.
Dakatarwar ta biyo bayan zarge-zargen amfani da ofis ba bisa ka’ida ba, wanda ya jawo korafe-korafe da dama daga jama'ar yankin.
Asali: Legit.ng