IYC: Rikicin Ribas Ya Dawo Sabo, Kungiyar Duniya Ta Kalubalanci Shugaban Riko
- Kungiyar Matasa Ijaw (IYC) ta duniya ta soki matakin sauke dukkan masu rike da mukaman siyasa da shugaban rikon jihar ya yi
- Rahotanni sun nuna cewa kungiyar IYC ta bayyana cewa wannan mataki tamkar danniya ne da kawo mulkin soja babu wani dalili
- Kungiyar ta bukaci a gaggauta janye dakatarwar da aka yi wa Siminalayi Fubara tare da dawo da dimokuradiyya a jihar Ribas
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Kungiyar Matasan Ijaw ta Duniya (IYC) ta soki matakin da mai mulkin rikon kwarya na Jihar Ribas, Ibok-Ete Ibas ya dauka na sauke mukarraban gwamnati a jihar.
Dakatarwar da Ibok-Ete Ibas ya yi ta shafi sakataren gwamnati, shugaban ma’aikata, kwamishinoni, shugabanni da membobin hukumomi, mashawarta na musamman.

Asali: Twitter
Rahoton The Cable ya nuna cewa sakataren kungiyar IYC ne ya yi magana kan matakin da Ibok-Ete Ibas ya dauka a madadin kungiyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakataren IYC, Maobuye Nangi Obu ya ce kungiyar ta ce matakin tamkar take hakkin al’ummar Ribas ne da kuma shigar da jihar cikin mulkin kama-karya.
IYC: "An kawo mulkin danniya a Ribas"
A cewar IYC, sauke mutanen ba komai ba ce illa wani yunkuri na karbe cikakken iko tare da kawar da doka da oda a jihar.
Kungiyar ta bayyana cewa matakin ya bar Jihar Ribas a hannun wasu ‘yan tsiraru da aka nada don amfanin kansu kadai.
Rahoton Channels TV ya nuna cewa sanarwar ta ce:
"Wannan mataki ya na da mummunan tasiri ga harkokin tsaro. Ta hanyar ware manyan jami’an gwamnati, ana iya haifar da rikici kuma ana iya jefa jihar cikin rudani.”
IYC ta jaddada cewa wannan mataki ba don kyautata tafiyar da gwamnati aka yi shi ba, illa don karfafa iko a hannun wasu tsiraru.
Matasa Ijaw sun bukaci a dawo da jami'an gwamnati
Matasa Ijaw sun yi kira ga al’ummar Jihar Ribas da su ki yarda da wannan mataki, domin ba wai don ci gaban jihar aka yi shi ba, sai don son zuciya.
A cewar sanarwar:
"Mun yi Allah wadai da wannan matakin kama-karya, kuma muna kira ga mutanen Ribas da su mike tsaye don yakar wannan take hakki.
"Jihar Ribas ba ta wani mutum daya ba ce, ita ce mallakin al’ummarta gaba daya."
Kungiyar ta bukaci a janye sauke mutanen nan take tare da dawo da cikakken tsarin dimokuradiyya a jihar Ribas.

Asali: Instagram
Sakon kungiyar IYC ga gwamnatin tarayya
IYC ta bukaci gwamnatin tarayya da sauran hukumomi su shiga cikin lamarin don hana afkuwar rikici.
A cewar kungiyar:
"Dole a dawo da dimokuradiyya, kuma mutanen Ribas ba za su bari a danne su ba. Ba za mu amince da juya jihar zuwa mallakin wasu tsiraru ba.”

Kara karanta wannan
2027: Ta fara tsami tsakanin ƴan adawa, burin Atiku da maganar yanki na son ta da kura
Yanzu dai ana sa ido don ganin ko gwamnatin tarayya za ta dauki matakin da IYC ke bukata ko akasin haka.
Dalilin ganin Wike da alkalin kotun koli
A wani rahoton, kun ji cewa kotun kolin Najeriya ya yi karin haske kan ganin alkalin da ya yanke hukuncin rikicin Rivers tare da Nyesom Wike.
Jama'a sun fara maganganu da suke nuna zargi kan alkalin ne bayan an fara rade radin cewa ya raka Nyesom Wike wajen taro a Calabar.
Asali: Legit.ng