Barau na Kara Barazana ga Abba a Kano, 'Yan Fim din Dadinkowa Sun Goyi Bayansa

Barau na Kara Barazana ga Abba a Kano, 'Yan Fim din Dadinkowa Sun Goyi Bayansa

  • Barau Jibrin ya karɓi baƙuncin wasu ‘yan fim na Kannywood daga gidauniyar Alheri Dadinkowa a majalisar tarayya
  • Gidauniyar, wacce ke da mambobi fiye da 320, ta yaba wa ayyukan Sanata Barau musamman na ilimi da noma
  • Sanatan Barau ya yi alkawarin yin aiki tare da su, yana mai jaddada goyon bayansa ga masana’antar fina-finai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi baƙuncin wasu fitattun ‘yan wasan Kannywood daga gidauniyar Alheri Dadinkowa a Abuja.

Gidauniyar, wacce ke karkashin jagorancin Dalhatu Musa Dakata da aka fi sani da Nuhu Kansila, na taimaka wa marasa galihu a jihar Kano.

Barau
Barau ya karbi 'yan fim din Dadinkowa zuwa tafiyarsa. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Legit ta gano haka ne a cikin wani sako da Sanata Barau Jibrin ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Bayan fama da jinya, shugabar karamar hukuma ta rasu a Ramadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Sanata Barau, jaruman sun bayyana cewa sun yaba da ayyukansa, kuma sun yanke shawarar mara masa baya.

'Yan fim sun yabi ayyukan Sanata Barau

Sanata Barau ya bayyana cewa gidauniyar, wacce ke da mambobi sama da 320, ta jinjina masa bisa kokarinsa a majalisa, musamman wajen gabatar da kudirori.

Daga cikin kudirorin da suka jinjina masa har da na kafa Hukumar Raya Arewa maso Yamma (NWDC) domin bunkasa yankin.

Barau ya jaddada goyon baya ga Ilimi

Baya ga batun NWDC, ‘yan fim din sun yaba da shirin Sanatan na bunkasa noma a Arewa maso Yamma ta hanyar Barau Initiative for Agricultural Revolution in the North West (BIARN).

Haka zalika, sun bayyana shirin tallafin karatu da yake bayarwa a matsayin wani gagarumin aiki da ke taimaka wa matasa da marasa karfi.

Barau ya yaba da kokarin ‘yan fim

Kara karanta wannan

Yadda Akpabio ya "murkushe" yan majalisa da suka ki amincewa da dokar ta-baci

Sanatan ya ce ya na matukar jin dadin yadda ‘yan fim din suka keɓe wani ɓangare na kudinsu domin taimaka wa marasa karfi, musamman a watan Ramadan.

Ya ce irin wannan tsari yana da matukar muhimmanci, kuma hakan na tafiya da manufofinsa na tallafa wa jama’a, musamman mabukata.

Sanata Barau Jibrin ya tabbatar da cewa zai yi aiki tare da ‘yan fim din, ya na mai cewa manufarsu ta taimakon jama’a ta yi daidai da tashi.

Ya kuma jaddada goyon bayansa ga masana’antar fina-finai ta Kannywood domin ta samu ci gaba da gogayya da takwarorinta a Najeriya da kasashen ketare.

Barau
Barau ya karbi masu sauya sheka a Abuja. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Barau ya bukaci a kiyaye addini da al’ada

Sanata Barau ya yi kira ga jaruman fina-finai da su kasance masu kiyaye koyarwar addinin Musulunci da al’adar Hausawa a duk abin da suke yi.

Kara karanta wannan

Awanni da nada sababbin hadimai, Abba ya ba su umarnin bayyana yawan kadarorinsu

Ya ce hakan zai taimaka wajen kare martabar masana’antar fina-finai tare da tabbatar da cewa ana koyar da tarbiyya mai kyau a cikin al’umma.

Pantami ya yi magana kan masarautar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Isa Ali Pantami ya yi magana kan yadda rikicin sarautar Kano ya ki karewa.

Malamin ya ce jihar Kano jagora ce a Arewacin Najeriya kuma saboda haka bai kamata a ce an samu iyayen kasa biyu a jihar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng