"40% Ake ba Shi," El Rufai Ya Zargi Uba Sani da Yin Kashe Mu Raba da Yan Kwangila
- Nasir El-Rufai ya zargi Gwamna Uba Sani da karɓar kaso 40% daga ƴan kwangila kafin ya amince ya ba su aiki a jihar Kaduna
- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ba haka gwamnatinsa ta yi ba, hasali ma bai cika haɗuwa da ƴan kwangilar da ake ba aiki ba
- El-Rufai ya ce ya kaucewa duk wasu harkokin cin hanci da rashawa ne ba don tsoron EFCC ko ICPC ba sai don tsoron Allah SWT
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sake jaddada cewa bai karɓi ko kwabo daga ƴan kwangila ba har ya sauka daga mulki a 2023.
El-Rufai ya ce a shirye yake kuma ba ya jin tsoron kowa domin bai taɓa ɗaukar ko kwandala daga asusun gwamnatin Kaduna ba a tsawon shekaru takwas da ya yi.

Kara karanta wannan
'Yadda Ribadu ya hada kai da ICPC domin kai ni kurkuku kafin zaben 2027' - El-Rufai

Asali: Facebook
Malam Nasir ya yi wannan furuci ne a wata hira da aka yi da shi a Freedom Radio Kaduna wadda Legit Hausa ta bibiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
El-Rufai ya zargi Uba Sani da karɓar 40%
Tsohon gwamnan ya kuma zargi gwamna mai ci, Sanata Uba Sani da yin kashe mu raba da ƴan kwangila kafin ya ba su aiki a Kaduna.
A cewarsa, a yanzu duk wanda za a ba kwangila sai ya ga gwamna kuma ya cire masa kaso 40% gabanin ya samu wannan aiki.
Nasir El-Rufai ya yi ikirarin cewa a gwamnatin yanzu, Uba Sani na kwasar takardun kwangila ya nufi Abuja, ya karɓi kason shi sannan ya miƙawa ƴan kwangila.
Yada ake kashe mu raba da Uba Sani
"A irin gwamnatinsu ta yanzu, mutum bai iya samun kwangila sai ya ga gwamna, sai ya ba gwamna kaso 40%, abin da Uba yake yi kenan, da takardun kwangila yake zuwa Abuja, ya na bayarwa ana ba shi kudi."
"Duk mun san abin da suke yi, kowa a garin nan ya na magana kan wannan, sun ɗauka haka muka yi a gwamnatinmu, ba haka muka yi ba, ba haka muka yi ba wallahi.
"Kuma ba wai mun ƙi yin haka ba ne don tsoron EFCC ko ICPC, a'a ko kaɗan ba haka ba ne, mun guje wa haka ne don tsoron Allah, me za su iya yi, an kama Bashir Saidu an kai shi kurkuku, ya mutu ne?"
- In ji El-Rufai.

Asali: Facebook
"Mu na jin tsoron Allah" - El-Rufai
Tsohon gwamnan ya ce gwamnatinsa ta kaucewa harkokin rashin gaskiya ne ba don tsoron EFCC ba sai don tsoron Allah Maɗaukakin Sarki.
Ya ce babu abin da wani ɗan adam zai iya maka matukar Allah bai kaddara faruwat hakan a rayuwarka ba.
El-Rufai ya ce da dama daga cikin ƴan kwangilar da aka ba aiki a gwamnatinsa ba su taɓa ganinsa ba, domin a cewarsa, babu wata hulɗa da za ta haɗa shi da su.
'Badakalar kudin kananan hukumomi'
A wani labarin, kun ji cewa Nasir El-Rufai ya zargi Gwamna Uba Sani da karkatar da kuɗin kananan hukumomi ta hanyar sayen kadarori a ƙasashen waje.
Malam El-Rufai ya bayyana kasashen uku da yake zargin Uba Sani na sayen kadarori da kudin kananan hukumomin Kaduna da aka turo daga tarayya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng